HausaTv:
2025-02-20@08:52:55 GMT

An Bude Babban Taron Kasa Na Nijar

Published: 15th, February 2025 GMT

A Nijar yau ne aka bude babban taron kasar, wanda zai tsara dokoki kan yadda za’a tafiyar da kasar a lokacin mulkin rikon kwarya na soji.

Shugaban Nijar Janar Abdourahamane Tiani ne ya kaddamar da taron a Yamai babban birnin kasar inda ake sa ran shafe kwanaki hudu ana tattaunawa.

Taron zai kuma bayar da shawara kan tsawon wa’adin gwamnatin rikon kwarya.

Taron ya samu halartar tsofaffin shugabannin kasar ciki har da Mahamadou Issoufou da tsofaffin shugabannin majalisar dokokin kasar da tsofaffin firaministoci na kasar da wasu baki daga Burkina Faso da Mali da wasu kasashen.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Trump Ya fadawa Turawa Kan Cewa Basa Cikin Tattaunawa Kan Tsagaita Wuta A Ukraine

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa kasashen Turai basa cikin tattaunawar tsagaita wuta a Ukraine. Jaridar Daily Mail ya bayyana cewa hankalin shuwagabannin kasashen turai ya tashi a lokacin da JD Vance mataimakin shugaba Trump ya fada masu cewa ba wani shugaba daga cikin shuwagabannin kasashen Turai da zasu halarci taron tsagaita wuta na Ukraine. Wannan labarin ya Eu ta kira taron gaggawa don tattauna wannan batun. Sannan Sir Keir Starmer ya kuma hanya zuwa Amurka da gaggawa. Mataimakin shugaban kuma yakadansa na musamman a kan shirin tsagaita wuta a Ukraine ya bayyanawa Ukrain kan cewa batun shigar Ukraine kungiyar tsaro da NATO bai da wani muhimmanci a wajen shugaba Trump a yanzu. Mr Vances ya bayyana hakane a taron tsaro da ke gudana a birnin Munich.  

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kungiyoyin Falasdinawa A Gaza Sun Bukaci Yin Taron Musamman Domin Dakile Batun Tilasa Wa Mutanen Gaza Yin Hijira
  • Gidauniyar Tunawa Da Sir Ahmadu Bello Za Ta Gudanar Da Taronta Karo Na 11 A Bauchi.
  • Hana Biza: Najeriya ta cancanci a girmama ta – Babban Hafsan Tsaro
  • Tinubu Ya Taya Babban Mai Tace Labarai Na LEADERSHIP, Ishiekwene Murnar Cika Shekaru 60
  • An Nuna Nezha 2 A Zama Na Musamman A Hedikwatar MDD Dake Birnin New York
  • Babban Kwamandan Sojojin Iran Ya Sanar Da Tsarin Sabunta Matakan Mayar Da Martani Kan Makiya
  • An Gudanar Da Taron Bita Na Yini 4 Ga Malaman Tafsiri Da Ke Babura
  • Iran Za Ta Aike Da Tawaga A Matakin Koli Don Halartar Jana’izar Nasrallah
  • Trump Ya fadawa Turawa Kan Cewa Basa Cikin Tattaunawa Kan Tsagaita Wuta A Ukraine
  • Shugaba Xi Ya Halarci Taron Kamfanoni Masu Zaman Kansu Tare Da Gabatar Da Jawabi