Iran Da Lebanon Sun Tattauna Kan Dangantakar Dake A Tsakaninsu
Published: 15th, February 2025 GMT
Kasashen Iran da kuma Lebanon sun tattauna kan dangantakar dake a tsakaninsu dama halin da ake ciki a yankin.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da yammacin yau Asabar, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na Lebanon din Youssef Raji sun jaddada muhimmancin mutunta juna da hadin gwiwa.
Iran da Lebanon suna da dangantaka mai karfi da ta dogara da muradu guda, tare da ci gaba da tattaunawa don karfafa hadin gwiwa a cikin kalubalen da ake fama da shi a yankin.
Araghchi ya taya Youssef Raji murnar nadin da aka yi masa a matsayin sabon ministan harkokin wajen Lebanon, tare da yi masa fatan samun nasara a sabuwar gwamnatin Lebanon.
Ya jaddada mahimmancin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta bangarori daban-daban da suka hada da siyasa, tattalin arziki, kasuwanci, da al’adu.
Ministocin sun kuma tattauna kan bukatar tattaunawa don warware batutuwan da suka shafi jigilar fasinjoji tsakanin kasashen biyu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jagora: Siyasar Kasar Iran Ta Ginu Ne Akan Kyautata Alaka Da Kasashen Makwabta
Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamnei wanda ya gana da sarkin Katar a jiya Laraba ya bayyana cewa; Siyasar Iran ta ginu ne akan kyautata alaka da kasashen makwabta, kuma tuni an cimma sabbin matakai a wannan fagen.
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma fada wa sarkin na Katar Tamim Bin Hamad ali-Sani cewa, ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci yana fadi tashi a wannan fagen na kyautata alaka da kasashen makwabta, tare da yin kira da cewa yarjeniyoyin da aka kulla su zama masu kare maslahar kasashen biyu.
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana kasar Katar a matsayin kasa abokiya, kuma ‘yar’uwa ta Iran, duk da cewa har yanzu da akwai wasu batutuwa da ba a kai ga warware sub a,kamar dawo da kudaden Iran da aka zuba a Bankunan kasar daga Korea Ta Kudu.
A nashi gefen sarkin Katar ya jinjinawa matakan da Iran din take dauka na taimakawa raunana a duniya, da kuma al’ummar Falasdinu, kuma yadda ta kasance a tare da Falasdinawa wani abu ne da ba za taba mancewa da shi ba har abada.