Kungiyoyi 70 Na Amurka Sun Bukaci Trump Ya Yi Watsi Da Shirinsa Kan Gaza
Published: 15th, February 2025 GMT
Kungiyoyin kare hakkin fararen hula da kungiyoyin fafutuka sama da 70 ne suka bukaci shugaban Amurka Donald Trump da ya yi watsi da shirinsa na kwace iko da yankin Zirin Gaza tare da tilastawa Falasdinawa kaura zuwa kasashe makwabta.
Wasikar da aka aike wa Donald Trump ta bayyana matukar damuwar kungiyoyin da suka sanya hannu kan shirin korar Falasdinawa kusan miliyan biyu daga kasarsu ta asali.
Wadanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sun yi kira ga gwamnatin Amurka mai ci da ta karfafa yunkurin diflomasiyya a baya da ya kai ga tsagaita bude wuta a Gaza, maimakon aiwatar da manufofin da za su kawo cikas ga yankin yammacin Asiya.
A cikin wasikar da suka fitar sun ce matakin na Amurka kan Gaza na iya haifar da martani mai karfi daga kasashen Larabawa da na musulmi, da jawo sojojin Amurka cikin sabbin yake-yake marasa iyaka, wanda hakan zai haifar da karin rikici a yankin.”
Wasikar ta bukaci Trump da ya yi aiki da abokan huldar yankin don sake gina Gaza ba tare da korar mazaunanta ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An gudanar da gagarumar zanga-zangar nuna goyon bayan Falastinu a kasar Jordan
Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Gaza.
A rahoton factjo, dubban mutane sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a wani gagarumin maci na wannan Juma’a.
Mahalarta tattakin sun yi Allah wadai da hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan.
A cikin wannan maci da aka gudanar bisa gayyatar Harkar Musulunci da kwamitin Tallafawa Falastinawa suka kira, dubban mutane sun halarta da suka hada da wakilai na siyasa, jam’iyyu, da kungiyoyin kwadago, da sauran jama’ar kasa, inda suka yi ta rera taken la’antar ayyukan zalunci na gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, da kuma kin amincewa da duk wata makarkashiyar da aka kulla domin korar Falastinawa daga yankunansu.
Haka nan Wadanda suka halarci tattakin sun yi Allah wadai da kisan kiyashin da ake ci gaba da yi a zirin Gaza, tare da yin kira ga gwamnatocin kasashen Larabawa da na Musulunci da su dauki matakin gaggawa na dakatar da wannan aika-aikar da Isra’ila ke yi.
Mahalarta tattakin na nuna alhinin shahadar Abu Hamza, kakakin rundunonin Quds Brigade, sun yaba da karfin azamarsa da jajircewarsa, da sadaukar da ransa da jininsa saboda ‘yancin al’ummarsa.
Masu zanga-zangar sun kuma yi Allah wadai da cin amanar Amurkawa, wadanda suka bai wa makiya yahudawan damar soke yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma ci gaba da kashe al’ummar Gaza, tare da bayyana gwamnatin Amurka a matsayin wadda take daukar nauyin wannan laifi ta hanyar aika bama-bamai da makamai masu linzami ga Isra’ila domin kisan Falastinawa a zirin Gaza.