Kanada Tana Adawa Da Sin Don Neman Tausayin Amurka Wadda Ta Kan Ci Zarafinta .

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Iran, ta yi Tir da kwamatin tsaro kan rashin tabaka komai na takawa Amurka da Isra’ila birki

Iran ta yi Allah wadai da Kwamitin Sulhun na MDD na rashin tabaka komai wajen  dakatar da ayyukan Amurka da Isra’ila wanda Iran din ta bayyana da abin kunya.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi tir da munanan hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan kasar Yemen da kuma yadda gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da kai wa Falasdinawa hari a zirin Gaza, tare da yin Allah wadai da rashin daukar wami mataki daga kwamitin sulhu na fuskantar wadannan munanan ayyukan.

Esmaeil Baghaei, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana matukar na dama kan yadda ake kashe fararen hula da suka hada da mata da kananan yara da ba su ji ba ba su gani ba, da kuma lalata muhimman ababen more rayuwa na kasar Yemen, sakamakon hare-haren da Amurka ke kaiwa.

Ya bayyana hare-haren da Amurka ta kai ta sama a matsayin laifukan yaki da laifukan ta’addanci, yana mai danganta hakan da “abin kunya da rashin gaskiya” na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da sauran cibiyoyin kasa da kasa kan wannan ta’asa.

Ya ce Amurka da gwamnatin yahudawan sahyoniya sun kitsa wani shiri na hadin gwiwa na raunana al’ummar musulmi da kuma rufe duk wata muryar goyon baya ga al’ummar Falastinu da ake zalunta.

Daga karshe Baghaei ya jaddada nauyin da ya rataya a wuyan kasashen musulmi na duniya na dakatar da zaluncin da Isra’ila ke yi da kuma hare-haren da sojojin Amurka suke yi a kan Falasdinawa da sauran al’ummar musulmi, yana mai kira ga gwamnatocin musulmi da su dauki matakin da ya dace da kuma kokarin da kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ke yi na shawo kan lamarin.

Akalla Falasdinawa 436 da suka hada da kananan yara 183 ne aka kashe tun bayan da Isra’ila ta keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza a ranar Talata.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [15]
  • Turkiya:Fiye Da’Yan Adawa 300,000 Su Ka Yi Zanga-Zanga Nuna Kin Jinin  Tayyib Ordugan
  •  Amurka: Turmp Yana Son Yin Yarjejeniya Ne Da Iran Ba Yaki Ba!
  • An yi wa wata karya tiyatar ceton rai
  • Putin Ya Aike Wa Ayatullah Khamenei Da Murnar Idin Nowruz
  • Iran da UAE sun kirayi Isra’ila da Amurka da su kawo karshen hare-harensu a Gaza da Yemen
  • Iran, ta yi Tir da kwamatin tsaro kan rashin tabaka komai na takawa Amurka da Isra’ila birki
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [13]
  • ’Yan adawa sun shirya ƙalubalantar Tinubu a zaɓen 2027 – Atiku
  • Mun Yi Watsi Da Ayyana Dokar Ta-Ɓaci Da Tinubu Ya Yi A Ribas – Shugabannin Adawa