Dalilin da ’yan siyasa ke sauya sheƙa zuwa APC — Tambuwal
Published: 15th, February 2025 GMT
Tsohon Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa guguwar sauyin sheƙa da ta fara kaɗawa a tsakanin jam’iyyun siyasa a Arewa maso Yammacin ƙasar na da alaƙa na son zuciyar ’yan siyasar yankin.
Tambuwal ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a taron ƙusoshin jam’iyyar PDP da ya gudana yau Asabar a Jihar Kaduna.
Tambuwal ya zargi ’yan siyasar da ke sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki a ƙasar da son zuciya waɗanda ya ce ba sa kishin al’umma.
Tsohon gwamnan ya ce akwai dalilai da ’yan siyasa ke sauya sheƙa daga wannan jam’iyyar zuwa wata, “sai dai abin da na fahimta shi ne galibi ’yan siyasar na yin hakan ne ba don kishin al’umma ba face sai don buƙatunsu na ƙashin kai.
“Sannan kuma a yanzu duk wani ɗan siyasar da ya san abin da ya kamata, ba zai koma jam’iyyar APC ba saboda ƙuncin rayuwa da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta jefa ’yan Nijeriya a ciki.
Tambuwal wanda ƙusa ne a jam’iyyar PDP a Nijeriya, ya caccaki Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin APC da cewa ba ta wata madafar kamawa ballanta sanin inda ta dosa haɗi da rashin tausayin ’yan ƙasar.
Sanatan Sakkwato ta Kudu ya yi kira ga duk jam’iyyun adawa a ƙasar da su haɗa ƙarfi domin kawo wa ’yan Nijeriya sauyin da suke buƙata a Zaɓen 2027.
Aminiya ta ruwaito cewa, daga cikin manyan ’yan siyasar da suka halarci taron akwai tsohon Gwamnan Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi da takwaransa na Kano, Sanata Ibrahim Shekarau da tsohon ɗan takarar Gwamnan Jigawa, Mustapha Sule Lamido da Sanata Lado Dan Marke, da Honarabul Isa Ashiri Kudan da Ango Abdullahi da Shugaban Matasa na PDP, Muhammad Kadade Suleiman da sauransu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Aminu Waziri Tambuwal zaɓen 2023 Zaɓen 2027 yan siyasar
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Iran Zata Aika Da Tawaga Mai Karfi Zuwa Jana’izar Sayyid Nasarallah
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’el Baghae ya ce gwamnatin kasar Iran zata aika tawaga mai karfi zuwa kasar Lebanon don halattar Jana’izar Sayyid Hassan Nasarallah wanda za’a gudanar a cikin yan kwanaki masu zuwa.
Bakha’I ya kara da cewa, zamu halarci Jana’izar a kasar Lebanon, kuma zamu aika da tawaka wacce zata kunshi manya-manyan jami’an gwamnati da kuma malaman addini.
A ranar Talatan da ta gabata ce wani jami’an kungiyar ta Hizbullah, ya bada sanarwan cewa baki daga kasashe 79 ne zasu halarci jana’izar.
Sheikh Ali Daher shugaba kwamitin gudnar da jana’izar ya kara da cewa, ranar zata kasashen ranar sabonta bai’a da marigayin da kuma wanda ya gaje shi.
A ranar 27 ga watan Satumba shekara ta 2024 ne jiragen yakin HKI suka sauke ton 85 da boma-bomai a kan shugaban kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah wanda ya kai ga rasa ransa..
annan bayan yan kwanaki suka kashe magajinsa, Sayyis Safiyuddeen.
A cikin watan Octoba ne sojojin yahudawan suka kashe Shahid Sayyid Safiyyud, amma za’a hada Jana’izar shuwagabannin biyu a rana guda, amma za’a rufe su a a wurare daban-daban.