Mazabar Tsanyawa/Kunchi ta shafe shekara guda ba tare da wakilci ba
Published: 16th, February 2025 GMT
Shekara guda bayan da Hukumar Zabe (INEC) ta dakatar da sake zaben mazabar Tsanyawa da Kunci a Majalisar Dokokin Jihar Kano, yankin ya ci gaba da zama babu zaɓaɓɓen wakili da yake wakiltar su a Majalisar Dokokin jihar.
Hukumar Zabe ta Ƙasa ta dakatar da sake zaɓen ne a ranar 3 ga Fabrairu, 2024, bayan da wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ce suka tarwatsa sake gudanar da zaben a wasu rumfunan zabe da dama a kananan hukumomin biyu.
A shekarar 2023 ce Kotun Daukaka kara ta soke zaben dan Majalisar Dokoki na Jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar, Alhaji Garba Ya’u Gwarmai, biyo bayan kalubalantar nasarar da ya samu a shari’a da Alhaji Yusuf Ali Maigado na Jam’iyyar NNPP ya shigar.
Kotun ta bayar da umarnin a sake yin zabe cikin kwanaki 90.
Da yake tsokaci kan rashin wakilcin da mazabar ta daɗe ba ta da shi, masanin harkokin siyasa, Dokta Kabiru Sufi ya ɗora alhakin lamarin ga Hukumar Zabe ta kasa da kuma ’yan siyasa da masu ruwa da tsaki daga mazabar, yana mai zargin su da gazawa wajen ganin an gudanar da zaben cikin lumana da kwanciyar hankali.
“Masu ruwa da tsaki a yankin suna da hujjar tambayar Hukumar Zabe ta kasa dalilin da ya sa ta gaza kammala aikin gudanar da zaben kamar yadda doka ta tanada,” in ji Dokta Sufi.
Wani mazaunin yankin Malam Muhammad Tsamiya ya koka da rashin samun wakilci, inda ya bukaci gwamnan jihar da ya tabbatar da cewa ba a yi watsi da mazabar ba, musamman ganin yadda take fama da rashin isassun kayayyakin more rayuwa.
“Kunci yanki ne mai nisa, inda hatta malaman da aka tura domin gudanar da aikin nan sun ki zuwa saboda ba mu da hanyoyi ga matsalar ruwan sha da dai sauran matsaloli.
“Don haka a siyasance, gwamna shi ne wakilinmu tun da jihar baki ɗaya mazabarsa ce,” inji shi.
Ya zuwa yanzu dai Hukumar Zabe INEC ba ta sanar da wata rana ba da za a sake gudanar da zaben ba.
Da wakilinmu ya tuntubi shugabar kula da sashen wayar da kan masu kada kuri’a ta Hukumar Zabe ta Kasa, Hajiya Safiya ta bayyana cewa, idan hukumar ta shirya lokacin gudanar da zaben, kwamishinan Hukumar Zabe ta kasa, Ambasada Abdu Zango zai kira taron masu ruwa da tsaki domin tattauna tsare-tsaren yadda za a gudanar da zaɓen.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Kano Zaɓe gudanar da zaben Hukumar Zabe ta
এছাড়াও পড়ুন:
Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce shirye-shirye sun yi nisa game da aikin Hajjin shekarar 2025 a jihar.
Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga Radio Nigeria a hedikwatar hukumar da ke Dutse.
A cewarsa, zuwa yanzu hukumar ta mika sunayen maniyyata fiye da dubu ɗaya da suka kammala biyan kuɗin aikin Hajji daga jihar zuwa ga Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON).
Ya ce tuni aka fara shigar da waɗanda suka kammala biyan kuɗin cikin tsarin neman biza.
Labbo ya bayyana cewa hukumar ta biya Hukumar Hajji ta Ƙasa kuɗi naira biliyan takwas a madadin alhazan jihar na shekarar 2025.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce ana gudanar da tarukan bita ga maniyyata a kullum, a kananan hukumomi 27 na jihar, ta hannun wasu malamai don ilmantar da su game da aikin hajjin.
Ya ƙara da cewa hukumar za ta raba jakunkuna da za su daukin nauyin kilo 8 da unifom ga jami’an yankuna da cibiyoyi domin rabawa mahajjatan.
Shugaban hukumar ya ja hankalin maniyyatan da su riƙa halartar traon bita saboda muhimmancinsa.
Ya yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa goyon baya da haɗin kai da yake ba hukumar domin samun nasarar gudanar da aikin hajji ba tare da wata tangarda ba.
Radio Nigeria ta ruwaito cewa Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ware kujeru sama da 1,800 ga jihar domin aikin hajjin bana.
Usman Muhammad Zaria