Mutum Biyu Sun Faɗa Komar ‘Yansanda Bisa Zargin Sata A Gombe
Published: 16th, February 2025 GMT
“A binciken da ake yi, an gano dukkan kayayyakin da aka sace bayan an sayar da su kan kudi naira 80,000, kuma wadanda ake zargin sun amsa laifin aikata laifin.”
PPRO ya kara da cewa, ‘yansanda na ci gaba da neman mutum na uku da ake zargi mai suna Ibrahim Danmariya, wanda ake kyautata zaton shi ne mai karbar kayan da aka sace.
“Muna kira ga jama’a da su bayar da bayanai masu amfani da za su kai ga kama wanda ake zargi da gudu.
“Muna tabbatar wa jama’a cewa za a yi amfani da duk bayanan cikin sirri,” in ji Abdullahi.
এছাড়াও পড়ুন:
Hamas Ta Sanar Da Shahadar Wani Jagoranta Da HKI Ta Kashe A Lebanon
Dakarun “Kassam” na kungiyar Hamas sun sanar da shahadar Muhammad Shahin wanda daya ne daga cikin kwamandojinta da ya yi shahada sanadiyyar harin da HKI ta kai masa a birnin Saida na kasar Lebanon.
Sanarwar ta dakarun “Kassam” ta ce, Muhammad Ibrahim Shahin wanda ake yi wa lakabi da Abul-Bara’a ya yi shahada ne a karkashin “Tufan-ak-Aksa” bayan da ‘yan mamayar HKI su ka yi masa kisan gilla a garin Saida dake kudancin Lebanon a jiya Litinin.
Har ila yau dakarun Kassam sun yi bayani akan rawar da shahidin ya taka a fagen gwgawarmaya da jihadi akan ‘yan mamaya, tun daga boren Intifada na Aksa, har zuwa farmakin guguwar Aksa.
Haka nan kuma bayanin na Kassam ya ce, Abul-Baraa ya riski dan’uwansa Shahin Hamzah Shahid wanda ya gabace shi da yin shahada da kuma sauran ‘yan’uwansa shahidai masu tsarki.
Kassam din ta yi alkawalin ci gaba da tafiya akan tafarkin shahidin na jihadi da gwagwarmaya har zuwa cimma manufofin al’ummar Falasdinu na ‘yanto da Falasdinu da fursunonin da suke kurkuku da kuma komawar Falasdinawa ‘yan hijira zuwa gida.