Jamus: Nahiyar Turai Tana Da Karfin Fuskantar Barazanar Amurka
Published: 16th, February 2025 GMT
Shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz ya gargadi Amurka da cewa, turai a shirye take ta kalubalanci barazanar da take yi mata, duk da cewa dai tana fatan fahimtar juna.
Shugaban gwamnatin kasar ta Jamus; Duk wanda yake son nahiyar turai ta shiga cikin batun zaman lafiya, to dole ne ya yi tarayya da ita cikin daukar matakan da su ka dace.
Shugaban gwamnatin na kasar Jamus dai yana mayar da martani akan batun kawo karshen yakin Rasha da Ukiraniya ba tare da bai wa kasashen na turai damar bayyana ra’ayinsu akan batun ba.
Dangane da batun kara kudaden fito akan hajar da kasashen turai ke shigarwa Amurka, Olaf Scholz ya ce, Turai tana da karfin da za ya iya fuskantar kowace irin barazana daga Amurka, akan kara kudin fito,’ tare da bayyana fatansa na ganin an kai ga fahimtar juna da zai hana a fada cikin yakin kasuwanci.
Shugaban gwmanatin kasar ta Jamus ya kuma ce; Idan har ya zamana babu wani zabi a gaban nahiyar turai sai mayar da martani, to tana da Karfin yin hakan acikin hadin kai.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Sudan Sun Kwace Iko Da Fadar Shugaban Kasa A Birnin Khartum
Sojojin Sudan sun sanar a yau Juma’a cewa sun kwace iko da fadar shugaban kasa dake tsakiyar birnin Khartum, bayan da su ka kori mayakan rundunar kai daukin gaggawa.
Majiyar ta ce, sojojin na Sudan sun fara da kutsawa cikin fadar shugaban kasar ne, ta mashigar gabas,bayan da su ka kashe mayakan rundunar kai daukin gaggawa da dama,yayin da wasu da dama su ka gudu zuwa cikin kasuwar dake kusa.
Bayanin da sojojin na Sudan su ka fitar ya kunshi cewa; Mun murkushe mayakan Duqlu, ‘yan ta’adda a tsakiyar birnin Khartum da kuma kasuwar Larabawa da ginin fadar shugaban kasa da sauran ma’aikatu.”
Har ila yau majiyar sojan na Sudan ta ce,su kuma yi nasarar rusa makamai da motocin yakin rundunar kai daukin ggagawar,kamar kuma yadda ta kame wasu masu maya.
Janar Nabil Abdullah wanda shi ne kakakin sojan na Sudan ya sanar da cewa; Za su ci gaba kai hare-hare a cikin dukkanin fagagen yaki har samun nasara.