Janar Musa ya fallasa ƙasashen da ke ɗaukar nauyin Boko Haram
Published: 16th, February 2025 GMT
Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya sake jaddada cewa ƙasashen waje ne ke tallafa wa ’yan ta’addan Boko Haram da kuɗi da makamai.
A wata hira da ya yi da Al Jazeera, Janar Musa ya nuna damuwa kan yadda ƙungiyar ke ci gaba da aikata ta’addanci sama da shekaru 16, duk da ƙoƙarin da sojojin Najeriya ke yi na daƙile.
Ya bayyana cewa an kama wasu ’yan Boko Haram ɗauke da maƙudan kuɗaɗe da ke da alaƙa da ƙasashen ƙetare.
Ya nuna cewa akwai ƙasashen da ke taimaka wa ƙungiyar daga waje.
Janar Musa ya yi tambaya cewar: “Ta yaya Boko Haram suka ci gaba da kai hare-hare tsawon shekaru 15?”
Bayanansa sun samu goyon baya daga wani ɗan majalisar dokokin Amurka, Scott Perry, wanda ya zargi hukumar USAID da bai wa ƙungiyoyin ‘yan ta’adda, ciki har da Boko Haram, tallafin dala miliyan 697 a kowace shekara.
Perry, ya ce akwai shaidun da ke nuna cewa kuɗaɗen da ake warewa wasu ƙasashen duniya don tallafa wa al’umma, kamar Pakistan da Afganistan, ba sa zuwa inda ya kamata, maimakon haka, ana amfani da su wajen ɗaukar nauyin ’yan ta’adda.
Bincike, ya nuna cewa an ware dala miliyan 136 don gina makarantu 120 a Pakistan, amma babu wata shaida da ke tabbatar da cewa an gina waɗannan makarantu.
A cewar Janar Musa, akwai buƙatar a binciki waɗannan kuɗaɗe da ake samu a hannun Boko Haram.
Ya ce: “Ina suke samun kuɗin? Wane ne ke ba su horo da makamai?”
Samun ’yan Boko Haram sama da 120,000 da aka kama ɗauke da kuɗaɗen ƙasashen waje ya haifar da tambayoyi masu yawa kan haƙiƙanin tushen ƙungiyar.
Janar Musa, ya jaddada cewa ikon Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare a Najeriya na nuna cewa suna samun tallafi daga ƙasashen waje.
Masana harkokin tsaro sun buƙaci gwamnati da sojojin Najeriya da su ƙara ƙaimi wajen bankaɗo waɗanda ke bai wa ’yan ta’adda goyon baya daga ƙetare.
Janar Musa, dai ya samu yabo kan yadda yake ƙoƙarin kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci a Najeriya, yayin da ya ke ci gaba da jagorantar sojojin ƙasar wajen yaƙi da ‘yan ta’adda.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram hare hare yan ta adda
এছাড়াও পড়ুন: