Gwamnatin Zamfara ta haramta taruka siyasa saboda tsaro
Published: 16th, February 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Zamfara ta haramta gudanar da tarukan siyasa a faɗin jihar har sai abin da hali ya yi, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Wannan mataki ya biyo bayan wasu tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa, inda jam’iyyar adawa ta APC ta koka cewa an kai wasu daga cikin jami’anta hari.
Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Zamfara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Al’amuran Jama’a, Mustafa Jafaru Kaura, ya bayyana cewa an ɗauki mataki ne, sakamakon wata hatsaniya da ta auku a Ƙaramar Hukumar Maru.
Ya ce: “Daga yanzu, an haramta duk wani taro ko gangami da zai iya haddasa tashin hankali, musamman ganin yadda aka rasa rayuka da ƙone dukiya mai yawa a Ƙaramar Hukumar.”
Ya kuma ƙara da cewa wannan dakatarwa ba ta dindindin ba ce, illa dai mataki ne na wucin gadi domin kiyaye zaman lafiya a jihar.
Martanin Jam’iyyar APCA nata ɓangaren, jam’iyyar APC reshen Zamfara, ta soki matakin, inda ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne saboda tsoron ƙarfin jam’iyyar a jihar.
Mai magana da yawun jam’iyyar, Malam Yusuf Idris Gusau, ya ce: “Ai abin mamaki ne a ce an hana tarukan siyasa, domin ba gangamin yaƙin neman zaɓe aka shirya ba.
“Babu wata doka da ta hana tarukan jam’iyyu, don haka gwamnati ba ta da hurumin hana mu gudanar da harkokinmu na siyasa.”
Ya ƙara da cewa APC jam’iyya ce mai rijista a ƙasa, kuma mabiyanta suna bin doka ba tare da haddasa wata fitina ba.
Fargabar Ƙarin Tashin HankaliAna dai ganin wannan mataki na gwamnati da martanin APC na iya ƙara dagula lamarin siyasa a jihar.
Masana da masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin akwai buƙatar a samu tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu, tare da shiga tsakani da dattawa da jami’an tsaro domin hana rikicin ya tsananta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: martani Siyasa Taruka Zamfara jam iyyar a
এছাড়াও পড়ুন:
Atiku ya jagoranci manyan ’yan siyasa sun ziyarci Buhari
Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a Kaduna.
Atiku ya samu rakiyar tsofaffin gwamnoni da suka haɗa da tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da tsohon Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da wasu jiga-jigan ’yan siyasa.
An gano gawar makiyayi da ƙwato shanu a Filato Boko Haram: Zulum ya yi ganawar sirri da Shugabannin sojojiKamar yadda aka wallafa bidiyon ziyarar a Shafin Atiku na Facebook, an rubuta cewa sun ziyarci Buharin, kuma sun sha dariya.
“A matsayina na Wazirin Adamawa, na tsaya domin gudanar da shagungulan Sallah a Adamawa, inda na wakilci Sarkin Adamawa, Lamiɗo Fombina a wasu shagulgulan.
“Yau kuma na kai ziyarar gaisuwar Sallah ga Muhammadu Buhari wanda ya shugabanci ƙasar a tsakanin 2015 zuwa 2023. Na ji daɗin ziyarar, saboda kamar yadda ya saba, ya yi ta ba mu dariya sai da haƙarƙarina suka yi zafi.” Cewar Atiku.