NAFDAC ta gano wajen da ake sabunta magungunan da suka lalalce a Abiya
Published: 16th, February 2025 GMT
Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta gano wani waje a Jihar Abiya da ake sake gyara da sabunta magungunan da suka lalace domin sayar wa jama’a.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook.
Gwamnatin Zamfara ta haramta tarukan siyasa saboda tsaro Gwamnatin Yobe Ta Ɗauki Jami’an Kiwon Lafiya 42 AikiHukumar ta ce an gano waɗannan magunguna a wasu gine-gine da ke garin Umumeje, a Ƙaramar Hukumar Osisioma Ngwa.
NAFDAC, ta ce wannan waje yana kusa da kasuwar Ariaria a Aba, cibiyar kasuwanci a jihar.
Hukumar ta bayyana cewa ta kai samame wajen ne tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro domin daƙile safarar jabun magunguna.
Wannan yana ɗaya daga cikin ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na kare lafiyar al’umma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Abiya
এছাড়াও পড়ুন:
Za Mu Bi Doka Domin Dawo Da Haƙƙinmu – Fubara
Fubara ya ƙara da cewa, duk da rikicin siyasar da ake fama da shi, gwamnatinsa tana ci gaba da aiki yadda ya kamata, kuma ana biyan ma’aikata albashinsu tare da ƙaddamar da muhimman ayyuka a jihar.
Ya buƙaci al’ummar jihar su ci gaba da bin doka da oda, yana mai cewa za su ci gaba da tuntuɓar hukumomin da suka dace domin tabbatar da cewa dimokraɗiyya ta ci gaba da ƙarfafa a jihar.
An fara samun matsala a siyasar Jihar Ribas tun bayan da rashin jituwa ya ɓulla tsakanin Fubara da tsohon gwamnan jihar, wanda yanzu shi ne Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike.
Rikicin ya kai ga cewa wasu ‘yan majalisar dokokin jihar masu biyayya ga Wike suka yi barazanar tsige Fubara daga muƙaminsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp