Mujallar “Qiushi” da aka buga a yau Lahadi, ta gabatar da muhimmin sharhi na sakatare janar na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping mai taken “Inganta tsarin daukar kwararan matakai wajen tafiyar da jam’iyya a dukkan fannoni”.

A cikin sharhin an nuna cewa, har yanzu ana fuskantar matsanancin yanayi da sarkakiya wajen yaki da cin hanci da rashawa, kuma jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin za ta dade tana fuskantar wannan jarrabawar.

Saboda haka, dole ne dukkan mambobin jam’iyyar a ko da yaushe su sa lura da nuna karfin zuci, da daukar kwararan matakai wajen tafiyar da harkokin jam’iyyar na dukkan fannoni, ta yadda za a iya raya jam’iyyar yadda ake bukata. Ban da haka, ya kamata mambobin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin su ba da misali, da hada kai tare da sauran ’yan jam’iyyar don kula da harkokin jam’iyyar da kyau, ta yadda za a ba da tabbaci ga gina kasa mai karfi da farfado da al’umma ta hanyar zamanintarwa irin ta kasar Sin. (Mai fassara Bilkisu Xin)

 

 

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: ta kasar Sin

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnati Ta Buƙaci Sauƙaƙa Tsarin Samar Da Biza Don ƙarfafa Kasuwancin ‘Yan Nijeriya A Duniya

Ya ce: “A bara, na wakilci Nijeriya a Indonesiya, kuma na gano cewa akwai manyan kamfanoni hamsin daga Indonesiya da ke aiki a Nijeriya, amma ba mu da ko kamfanoni biyar daga Nijeriya da ke aiki a Indonesiya.

 

“Idan suna son zuwa ƙasar mu su yi kasuwanci saboda yawan mutanen mu da kuma damar da muke da ita na sayen kayayyakin su da ayyukan su, to ya kamata a samar da tsarin da zai ba da dama ga kamfanonin Nijeriya su ma. Matsalar ba da biza ga ‘yan Nijeriya na nan a Indonesiya da Habasha.”

 

Dangane da matsalar da ‘yan Nijeriya ke fuskanta bayan da gwamnatin Habasha ta soke tsarin nan na ‘e-visa’ da ‘Visa-on-Arrival’ ga matafiya daga Nijeriya, Idris ya tabbatar da cewa za a ɗauki matakin diflomasiyya ta hannun Ministan Harkokin Waje don magance matsalar.

 

Ministan ya bayyana cewa manufofin ba da biza a tsakanin ƙasashe na tafiya ne bisa tsarin da ke bai wa kowanne ɓangare dama daidai.

 

Ya ce ya zama dole ƙasashe su kasance masu adalci wajen aiwatar da manufofin da za su amfanar da ‘yan ƙasar su da na ƙasashen da suke hulɗa da su.

 

Ya ce: “Duk wata dangantaka da ƙasashen waje tana tafiya ne bisa tsarin amfanin juna. Idan muna ba su ‘Visa-on-Arrival’, babu dalilin da zai sa su hana mu ‘Visa-on-Arrival’.”

 

Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da ke zaune a ƙasashen waje da su kasance jakadu nagari, su nuna halaye nagari domin inganta sunan ƙasar.

 

“Ba ma yarda da mutanen da za su ɓata mana suna. Kuna da rawar da za ku taka, saboda ku ne ke zaune a nan. Idan ba ku wakilce mu da kyau ba, ba za a girmama mu ba. Ba wai ziyarar Shugaba Tinubu ko wani minista ce za ta gyara abin ba, amma ‘yan Nijeriya da ke zaune a nan ne za su iya gyara yadda duniya ke kallon ƙasar mu,” inji shi.

 

Idris ya kuma yi bayani kan sababbin manufofin da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa, inda ya ce an samu cigaba mai kyau a fannin farfaɗo da tattalin arziki, inganta ababen more rayuwa, yaƙi da rashin tsaro, da kuma dawo da ƙwarin gwiwar masu zuba jari a Nijeriya.

 

Ya ce Nijeriya ta samu jarin ƙetare na kusan dala biliyan 1.07 don kafa masana’antu da za su ƙera magunguna, matakin da zai taimaka wajen bunƙasa masana’antar magunguna a ƙasar, samar da ayyukan yi, da kuma ƙarfafa ɓangaren kiwon lafiya.

 

Haka nan, Ministan ya bayyana cewa a cikin kwanaki ƙasa da 250, an raba sama da naira biliyan 32 ga ɗalibai ƙarƙashin Shirin Lamunin Ɗalibai, domin tabbatar da cewa kowa na samun damar karatun boko ba tare da matsalar rashin kuɗi ba.

 

Dangane da ƙoƙarin yaƙi da rashin tsaro, Idris ya ce a shekarar 2024 kaɗai, jami’an tsaro sun kashe ‘yan ta’adda da ‘yan fashi 8,000, sun ceto mutane 8,000 da aka yi garkuwa da su, tare da cafke mutane 11,600 da ake zargi da aikata laifuka.

 

Har ila yau, ya tabbatar da cewa an kawar da ‘yan ta’adda daga hanyar Kaduna zuwa Abuja, wadda a da wurin aikata miyagun laifuka ce, lamarin da ya kawo sauƙi ga matafiya.

 

Da yake jawabi, Shugaban Al’ummar Nijeriya da ke Habasha, Muideen Alimi, ya ce suna shirin yin haɗin gwiwa da Hukumar Kula da ‘Yan Nijeriya Mazauna Ƙetare (NIDCOM) don shirya taron tattaunawa kan bunƙasa tattalin arziki ta hanyar kasuwanci tsakanin ƙasashen Afirka.

 

Ya buƙaci Nijeriya da ta goyi bayan shirin samar da Babban Bankin Afirka, tare da tabbatar da cewa Nijeriya ta taka muhimmiyar rawa a Hukumar Harhaɗa Kuɗaɗen Afirka (African Remittance Agency).

 

Taron ya samu halartar Darakta Janar ta Hukumar NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa, da wasu manyan jami’an gwamnati.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Turkiya Ta Karbi Bakuncin Tattaunawar Sulhu Tsakanin Habasha Da Somaliya
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa; Yahudawan Sahayoniyya Sun Kasa Murkushe Gwagwarmaya
  • Juyin-juya-halin Kyautata Muhalli: Rawar Da Kasar Sin Ke Takawa Wajen Samar Da Makoma Mai Kyau
  • Kasar Sin Ta Mayar Da Martani Ga Tattaunawar Amurka Da Rasha Kan Rikicin Ukraine
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Irin Gagarumar Rawar Da Iran Ta Taka A Fegen Tsaro Yakin Tekun Pasha
  • Ministan Harkokin Waje Iran Ya Jaddada Cewa Iran Ba Zata Tattauna Da Amurka A Karkashin Takunkumai ba
  • Kasar Sin: Yankin Asiya Da Tekun Pasifik Ba Wajen Kartar Kasashe Masu Karfin Iko Ba Ne
  • Gwamnati Ta Buƙaci Sauƙaƙa Tsarin Samar Da Biza Don ƙarfafa Kasuwancin ‘Yan Nijeriya A Duniya
  • Gwamnati ta kashe N5bn domin bai wa mata tallafin kiwon awakai a Katsina
  • Hukumar Kula Da Ayyukan Duba-gari Ta Kasa Za Ta Karrama Shugaba Tinubu