Kungiyar Tarayyar Afirka Ta Yi Tofin Allah Tsine Kan Shirin Korar Falasdinawa Daga Gaza
Published: 16th, February 2025 GMT
Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi Allah Wadai da duk wani Shirin tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga muhallinsu
Batun neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga kasarsu ta gado yana ci gaba da fuskantar tofin Allah da Allah wadai a duk fadin duniya da kuma a taruka daban-daban, kuma batun Falasdinu shi ne kan gaba a ajandar taron kolin Afirka karo na 38 da aka yi a birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar Habasha.
A yayin bude zaman taron kolin kungiyar tarayyar Afirka, shugaban hukumar Tarayyar Afirka, Moussa Faki, ya yi gargadi game da kiraye-kirayen da ake yi na tilastawa Faladinawa gudun hijira, yana mai jaddada cewa ci gaba da tauye wa Falasdinawa ‘yancinsu abin kunya ne ga bil’Adama, yana mai sukar shirun da kasashen duniya suka yi dangane da halin da ake ciki a Gaza da kuma jaddada ci gaba da goyon bayan kungiyar Tarayyar Afirka ga Falasdinawa. Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka Moussa Faki ya ce: Sun ga yadda duniya ta yi shiru duk da wannan mummunan yanayi da al’ummar Gaza ke ciki, har ma wasu daga cikinsu na yin kira da a kori Falasdinawa daga muhallinsu, lamarin zai kara ta’azzara mummunan kangin da Falasdinawa suka shiga.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: a Falasdinawa
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Irin Gagarumar Rawar Da Iran Ta Taka A Fegen Tsaro Yakin Tekun Pasha
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Iran tana taka rawa ta musamman wajen wanzar da kwanciyar hankali da tsaron yankin Tekun Pasha
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta hanyar mallakar mafi yawan layukan kan iyaka da tekun Pasha da kuma iko da mashigar Hormuz, ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali da tsaron wannan ruwa da yankunan makwabtanta.
Abbas Araqchi ya bayyana hakan ne a yayin taron tarihin huldar kasashen waje na Iran karo na 8, mai taken “Manufar harkokin wajen Iran da gabar tekun Pasha a cikin mahallin tarihi,” wanda aka gudanar a safiyar yau Talata a cibiyar nazarin siyasa da kasa da kasa na ma’aikatar harkokin wajen kasar: Tun daga tsawon tarihi har zuwa yanzu, yankin Tekun Pasha, yana matsayin daya daga cikin muhimman bangarorin ruwa a duniya, kuma yana daya daga cikin muhimman yankuna da suka shafi ci gaban rayuwar bil’adama, da muhimman tsare-tsare a fuskar mahanga daban-daban na bangarorin rayuwar dan Adam, wannan yanki na tekun Pasha yana nan a tunanin bil-Adama kuma ya cancanci matsayi da kulawa da bincike daga bangarori daban-daban.