Iran Da Iraki Sun Jaddada muhimmancin Tsaron Kan Iyakokin Kasashensu
Published: 16th, February 2025 GMT
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran ya ce: Tuntubar juna tsakanin Iran da Iraki ya zama wajibi don inganta matakan tsaro tsakanin kasashen biyu
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran kan harkokin siyasa Majid Takht Rawanji ya jaddada da cewa: Ziyarar da ya kai zuwa Iraki ta zo ne bisa tsarin tuntubar juna ta fuskar siyasa da aka saba yi tsakanin kasashen biyu.
Rawanji ya kara da cewa: Iran da Iraki sun tattauna kan batutuwan da suka shafi tsaro tsakaninsu a matsayinsu na kasashen ‘yan’uwa da musulmi, tare da jaddada muhimmancin hadin kai da hadin gwiwa don tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Ya kara da cewa, tsaron yankin shi ne babban fifiko ga kasashen Iran da Iraki, wanda ya bukaci ci gaba da tuntubar juna da kuma yin aiki tare a matakai daban daban na kasashen biyu.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Iran da Iraki
এছাড়াও পড়ুন:
Syria: SOHR ta fallasa jami’an tsaron sabuwar gwamnati na yi tsiraru kisan gilla
Kungiyar da ke sa ido da kare hakkin dan adam ta Syria (SOHR) ta fitar da fayafan bidiyo guda hudu da ke dauke da hotunan azabtarwa da kisa da jami’an tsaron sabuwar gwamnatin kasar karkashin kungiyar Tahrir Sham suke aiwatarwa a kan fararen hula tsiraru marasa rinjaye a kasar.
Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama a Syria ta bayyana a ranar Lahadi cewa, ta samu faifan bidiyo guda hudu ne da ke nuna yadda ake aiwatar da hukuncin kisa kan wasu matasa da ba sa dauke da makamai daga ‘yan Alawiyya, da jami’an tsaro suka aiwatar a kauyen al-Shir da ke yankin Latakia a ranar 7 ga watan Maris.
A cewar kungiyar, faifan bidiyon ya kara tabbatar da yadda aka aiwatar da kisan gillar da aka yi a yankunan gabar tekun Syria da kuma wadanda suka aikata hakan a kan fararen hula.
A cikin faifan bidiyo na farko ya nuna wasu matasa biyu sun durkusa a kasa yayin da jami’an tsaron sabuwar gwamnatin Syria suke zaginsu tare da lakada musu matsanancin duka, duk kuwa da ikirarin da suka yi na cewa ba su aikata wani laifi ba.
A cikin wani faifan bidiyo na biyu, an nuna yadda aka azabtar da wasu fararen hula hudu ciki har da tsofaffi biyu, da kuma tilasta wa daya daga cikinsu sumbaci takalmin wani jami’in tsaro.
Kaset na uku ya nuna irin mumunan duka da aka yi wa fararen hula da bindigogi da karafa kafin daga baya kuma duk aka kashe su.
Dukkanin wadanda suka aikata wadannan munannan laifuka dai sabbin jami’an tsaron sabuwar gwamnatin Syria ne da kungiyar Tahrir Sham mai dangantaka da kungiyar Alqaida ta kafa a Syria bayan hambarar da gwamnatin Bashar Assad.