Shirin ACRESAL Na Jihar Jigawa Zai Samar Da Fitilu Akan Titunan Garuruwa 6
Published: 16th, February 2025 GMT
Shirin Inganta Muhalli da Samar da Ruwan sha da kuma bunkasa aikin gona ACRESAL a jihar Jigawa yace zai zabo garuruwa masu wahalar shiga guda 6 domin sanya musu fitilun kan titi masu amfani da hasken rana.
Shugaban shirin na jihar Jigawa, Alhaji Yahaya Muhamamad Uba Kafin Gana ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse, babban birnin Jihar.
Yana mai cewar, a yanzu haka ma tuni an zabi karin wasu garuruwa 60 domin basu bashin kudi marar ruwa.
A don haka, ya bukaci wadanda aka baiwa bashin a baya da su tabbatar sun biya domin wasu su amfana.
Alhaji Muhammad Uba yace Gwamna Umar Namadi ya amincewa shirin ACRESAL sayo karin injinan yashe kogi guda 2, wadanda za a rika amfani da su wajen yashe kogin Hadejia, domin samun saukin sarrafa ruwan kogi don hana ruwa shiga gonaki.
A cewarsa, ACRESAL da ma’aikatar kare muhalli ta jihar za su reni dashen itatuwa miliyan biyar da dubu dari biyar a bana, domin yaki da zaizayar kasa.
Shugaban shjirin na ACRESAL ya kara da cewar a yanzu haka ACRESAL tana gudanar da biyan diyyar naira miliyan 187 ga wadanda aikin zaizayar kasa ya shafi kadarorinsu a unguwannin Dan Masara da kuma Kalgo dake karamar hukumar Dutse.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Yobe na ciyar da almajirai a Tsangayu 85 kullum
Gwamnatin Jihar Yobe ta kafa cibiyoyin bayar da abinci 85 domin samar wa almajirai abinci a dukkanin Ƙananan Hukumomin 17 na jihar, a lokacin azumin Ramadan.
Sakataren zartarwa na Hukumar Ilimin Larabci da Addinin Musulunci ta Jihar Yobe, Malam Umar Abubakar ne, ya bayyana hakan a wata hira da Daily Trust a ranar Alhamis.
Sanƙarau ta kashe mutum 55 saboda rashin tsafta a Kebbi Dabarun Rabauta Da Kwanaki 10 Na Ƙarshen Ramadan“Muna bai wa makarantun Tsangaya 85 kayan abinci 85, biyar a kowace Ƙaramar Hukuma, inda muke ciyar da almajirai tsakanin 300 zuwa 400 a kowace makaranta,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa Gwamna Mai Mala Buni ne, ya amince da wannan shiri domin tallafa wa yara marasa galihu a jihar.
Baya ga haka, gwamnatin ta buɗe manyan cibiyoyin ciyarwa guda uku a Damaturu domin ciyar da sama da almajirai 2,000 da wasu mabuƙata.
Abubakar, ya bayyana cewa hukumar na kuma samar wa almajiran kayan sakawa.
“Mu na da alhakin tabbatar da cewa waɗannan yara sun ji cewa suna cikin al’umma.
“Zuwa yanzu mun ɗinkawa sama da 850 daga cikinsu tufafi, kuma Insha’Allah, muna da shirin ƙara wannan adadi a nan gaba,” in ji shi.
Ya gode wa gwamnan saboda goyon bayansa tare da kira ga sauran gwamnatoci da masu hali da su taimaka wajen tallafa wa yara marasa ƙarfi a cikin jama’a.