Leadership News Hausa:
2025-03-23@03:35:15 GMT

Adadin Kuskuren Da VAR Take Tafkawa Ya Ragu A Wannan Kakar

Published: 16th, February 2025 GMT

Adadin Kuskuren Da VAR Take Tafkawa Ya Ragu A Wannan Kakar

Masu lura da gasar sun ce kwarewar na’urar wajen yanke hukunci ya karu zuwa kashi 96.4 idan aka kwatanta da kashi 95.7% a kakar da ta gabata.

“Babu wanda yake shakku kan tasirin da ko da kuskure daya wajen yanke hukunci zai yi,” in ji wani babban jami’in kwallon kafa, Tony Scholes.

Ya ci gaba da cewa “Mun san cewa kuskure daya tal zai iya cutar da kungiya.

Sakamako da kuma makin da kungiya ke samu na iya sanyawa a kori mai horarwa ko kuma dan wasa ya rasa damarsa a cikin kungiya.”Hakan ya faru ga Erin ten Hag – domin daya daga cikin kurakurai hudu da na’urar VAR ta tafka shi ne bai wa West Ham bugun fanareti a wasa na karshe da kocin ya jagoranci kungiyar Manchester United.

Haka nan wasu alkalan wasan sun fuskanci cin zarafi, inda a kwanakin nan ‘yansanda suka kaddamar da bincike kan “barazanar cin zarafi” kan alkalin wasa Michael Oliber bayan wasan da Arsenal ta yi nasara kan Wolbes da ci 1-0 a watan Janairu. Kuma wannan ya biyo bayan matakin da alkalin wasan ya dauka na bai wa dan wasan Arsenal, Myles Lewsi-Skelly katin kora – matakin da daga baya aka soke bayan korafin da kungiyar ta shigar.

Shi ma tsohon alkalin wasa Dabid Conte, an kore shi ne a watan Disamba bayan binciken da aka gudanar a kansa. Hukumomin gasar Premier dai ba su bayyana lokuta 9 da na’urar VAR ta ki soke wani mataki ba – kuma babu tabbas ko batun jan katin da aka bai wa Lewis-Skelly na ciki amma hukumar ta yi bayani kan kurakurai hudu da na’urar ta tafka ga manema labarai.

Kuskure hudu da VAR ta tafka

Outtara ya ‘taba kwallo da hannu’ – Bournemouth 1-1 Newcastle, 25 ga Agusta.

Abin da ya faru: Dango Outtara ya zaci cewa ya ci wa kungiyarsa Bournemouth kwallon da za ta ba ta nasara lokacin da ya zura kwallon da kai. Lafari Dabid Coote ya bayar da kwallon.

Matakin VAR: Mai kula da na’urar VAR a wasan, Tim Robinson ya bai wa Coote shawarar soke kwallon, inda ya ce an taba kwallon da hannu. Kasancewar yana da yakini kan hukuncinsa, bai bukaci lafari ya kalli bidiyon lamarin ba.

Sakamako: Kasancewar babu cikakkiyar hujjar da za ta tabbatar da cewa kwallon tabbas ta taba hannun Ouattara, shugaban hukumar lura da alkalan wasan gasar Premier, Howard Webb a lokacin da ya tattauna da kafar yada labarai ta Sky Sports, ya ce – VAR ta yi kuskure wajen soke cin kwallon.

 

De Ligt ya kwashe Ings – West Ham 2-1 Man Utd, 27 ga Oktoba

Abin da ya faru: Xan wasan gaba na West Ham, Danny Ings ya fadi a cikin yadi na 18 lokacin da yake fafutikar buga kwallo tsakaninsa da mai tsaron baya na Manchester United, Mathijs de Ligt. Lafari Dabid Coote ya bayar da damar a ci gaba da wasa amma sai mai kula da na’urar VAR, Michael Oliber ya bukaci a sake dubawa a talabijin na gefen fagen wasa.

Matakin VAR: Daga nan ne Coote ya bayar da bugun fanareti, wanda dan wasa Jarrod Bowen ya zura a raga, kuma hakan ya bai wa West Ham nasara a wasan.

Sakamako: Washegari United ta sallami Ten Hag daga aiki. Daga baya Web ya ce bai kamata a bayar da fanaretin ba.

 

Jan katin da aka bai wa Norgaard – Brentford 0-0 Eberton, 23 ga Nuwamba

Abin da ya faru: Xan wasan Brentford, Christian Norgaard ya tokari mai tsaron ragar Eberton, Jordan Pickford a gwiwa lokacin da suke fafutikar kaiwa ga kwallo a cikin yadi na 18.

Mataki VAR: Alkalin wasa Chris Kabanagh bai ce an yi keta ba amma sai mai kula da na’urar VAR ya bukace shi ya sake duba wurin a talabijin din gefen fage. Bayan sake dubawa, nan take ya daga wa Norgaard jan kati.

Sakamako: Kwamiti mai zaman kansa ya soke dakatarwar da aka yi wa Norgard na wasa uku bayan korafi da kungiyar ta Brentford ta shigar.

Soke kwallon da Milenkobic ya zura – Nottingham Forest 3-2 Southampton, 19 ga Janairu.

Abin da ya faru: Nikola Milenkobic ya jefa kwallo a raga da kai inda hakan ya sanya Nottingham Forest ta yi gaba da ci 4-1.

Matakin VAR: Na’urar VAR ta umarci lafari Anthony Taylor ya soke cin saboda dan wasan Forest, Chris Wood ya yi satar fage inda hakan ya hana masu tsaron baya na

Southampton damar kalubalantar kwallon. Wood bai taba kwallon ba.

Sakamako: Kwamiti mai zaman kansa da ya duba lamarin ya ce ya kamata a bayar da cin.

Shin Ko Barcelona Ce Matsalar Dembele?

Tauraruwar dan wasa Ousmane Dembele tana ci gaba da haskawa tun bayan barinsa kungiuar kwallon kafa ta Barcelona inda ya ci gaba da saka kwazo a cin kwallaye, bayan da Paris St-Germain ta je har gida ta doke Brest 3-0 a wasan cike gurbi a Champions League ranar Talata inda Dembele ya zura kwallo biyu a raga karo na 10 yana cin kwallaye a jere a PSG, kuma na 18 jimilla a wasa 11 baya a dukkan fafatawa.

Xan wasan tawagar Faransa ya ci uku rigis a gasar zakarun Turai da Stuttgart kuma a tarihi wasu ‘‘yan wasa kadan ne da suka zura kwallo uku rigis a wasa biyu a jere a Champions League da ya hada da Lionel Messi a Barcelona a 2016 da Cristiano Ronaldo a Real Madrid a 2017.

Dembele bai samu kafa wannan tarihin ba, wanda aka sauya shi da Goncalo Ramos a minti na 82 a fafatawar. Kenan Dembele ya ci kwallo 14 a Ligue 1 da Champions League a 2025.

Tun kafin Dembele ya zura biyu a ragar Brest, Vitinha ne ya fara ci a bugun fenariti a minti na 21 da fara wasan kuma wannan shi ne wasan farko zagayen cike gurbi a sabon fasalin Champions League, za su kara a wasa na biyu a Paris ranar 19 ga watan Fabrairu. PSG, wadda ba ta taba daukar Champions League ba, an kusan fitar da ita a gasar bana a cikin rukuni, daga baya ta kara kwazo da ta doke Manchester City da Stuttgart a wasanninta na gaba.

Ana sa ran PSG za ta kai zagayen gaba cikin ruwan sanyi, wadda ake sa ran watakila ta fuskanci Liberpool ko kuma Barcelona a zagayen ‘yan 16.

 

 

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Var

এছাড়াও পড়ুন:

Kungiyar M-23 Ta Kasar Kongo Ta Kara Nusawa Gaba A Don Mamaye Karin Yankuna A Gabacin Kongo

Yan tawayen M-23 na kasar Kongo wadanda suke samun goyon bayan gwamnatin kasar Ruwanda sun kara nosawa zuwa gaba a mamayar da sukewa gabancin kasar ta Kongo.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa yan tawayen sun kama garin Walikale a jiya Laraba kuma a halin yanzun sun kokarin zuwa sauran garuruwa a yankin.

Labarin ya kara da cewa wannan labarin na zuwa ne a dai dai lokacinda shuwagabanninkasashen Kongo da Rwanda suke kira ga bangarorin biyu su tsagaita budewa juna wuta su kuma dawo kan teburin tattaunawa.

Wani mazaunin garin walikale ya fadawa reuters yana jin karar bindigogi a garin Nyabangi wanda yake kusa da inda yake.

Janvier Kabutwa yace, yan tawayen sun afafatawa da sojojin Gwamnati da kuma sojojin sa kai a garin bayan da mayakan M-23 suka tunkari sansanin sojojin gwamnati a garin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fadin Yankin Da Ke Fama Da Zaizayar Kasa Na Kasar Sin Ya Ragu A 2024 
  • Chelle Ya Fara Da Ƙafar Dama A Super Eagles 
  • An gudanar da gagarumar zanga-zangar nuna goyon bayan Falastinu a kasar Jordan
  • Iran da UAE sun kirayi Isra’ila da Amurka da su kawo karshen hare-harensu a Gaza da Yemen
  • Gwamnatin Bauchi Ta Ɗage Hawan Daushe Na Sallar Bana
  • Sallah: Tinubu Ya Raba Wa ’Yan APC Buhun Shinkafa 7,000 A Zamfara
  • Hauhawar Farashi A Nijeriya Ta Ragu Zuwa 23.18 Cikin 100 A Fabrairu — NBS
  • Xi Ya Bukaci A Bude Sabbin Hanyoyin Samun Ci Gaba Yayin Rangadinsa A Lardin Yunnan
  • Kungiyar M-23 Ta Kasar Kongo Ta Kara Nusawa Gaba A Don Mamaye Karin Yankuna A Gabacin Kongo
  • Jakadan Amurka Ya Ziyarci Sarkin Zazzau Domin Karfafa Alakar Amurka Da Najeriya