Aminiya:
2025-02-20@09:10:47 GMT

An tsinci gawar ɗan sanda a Otal a Ogun

Published: 16th, February 2025 GMT

An tsinci gawar wani Sufeton ’Yan Sanda, mai suna Haruna Mohammed, a cikin wani ɗakin otal a Jihar Ogun.

Marigayin, wanda ke aiki da Hedikwatar ’Yan Sanda ta Ishashi a Jihar Legas.

NAFDAC ta gano wajen da ake sabunta magungunan da suka lalalce a Abiya Gwamnatin Zamfara ta haramta tarukan siyasa saboda tsaro

Ya je otal ɗin Super G Royal da ke rukunin gidaje naAnthony Uzum tare da wata mata da misalin ƙarfe 1:00 na daren ranar Asabar.

Da misalin ƙarfe 8:52 na safiyar washegari ne, manajar otal ɗin, Deborah Adejobi, ta gano cewar ɗakin da suka kama ba a kulle yake ba.

Lokacin da ta shiga, sai ta tarar da ɗan sandan a kwance babu rai, kuma matar da suka zo tare ba ta cikin ɗakin.

Rahoton ’yan sanda ya bayyana cewa mamallakin otal ɗin, Abiodun Olagunju ne, ya kai rahoto ga hukumomi.

Ya kuma bayyana cewa matar da ta tsere ta je wajen masauƙin baƙi da misalin ƙarfe 6 na safe, inda ta nemi ruwan sha.

An ɗauke gawarsa zuwa ɗakin ajiyar gawa na Life Channel Mortuary da ke Olambe.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Ogun, Omolola Odutola, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Ta ce da farko ba gano ɗan sanda ba saboda ba a samu katin shaidarsa ba, sai bayan da aka bincika aka gano yana aiki da Hedikwatar ‘Yan Sanda ta Ishashi da ke Legas.

’Yan sanda sun fara neman matar da ta tsere, kuma ana ci gaba da bincike don gano dalilin mutuwarsa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ɗan Sanda Gawa

এছাড়াও পড়ুন:

Hana Biza: Najeriya ta cancanci a girmama ta – Babban Hafsan Tsaro

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya gargaɗi ƙasashe cewa Najeriya ba za ta yarda da rashin girmamawa daga kowace ƙasa ba.

Ya bayyana hakan ne bayan da Ƙasar Kanada ta hana wasu jami’an sojin Najeriya takardae izinin shiga ƙasar, duk da cewa an gayyace su don halartar wasannin Invictus a Vancouver.

’Yan bindiga sun Kashe mutum 2 kan jinkirin biyan kuɗin fansa Gwamnatin Gombe ta horar da makiyaya kan sabbin hanyoyin kiwo

Da yake jawabi a Hedikwatar Tsaro da ke Abuja, bayan tarbar sojojin da suka halarci gasar, Musa ya nuna takaicinsa kan yadda ake nuna wa ‘yan Najeriya rashin adalci a wasu ƙasashe.

“Mun bi dukkanin matakan da suka dace. An aiko mana da gayyata, jami’an gwamnati sun sani, kuma mun cika dukkanin sharuɗa.

“Amma, ba san dalilin da ya sa aka hana jagororin tawagarmu kamar kaftin, likitan tawaga da mai duba biza. A. Tambayar ita ce, me ya sa?” in ji shi.

Musa ya jinjina wa sojojin da suka wakilci Najeriya a gasar, inda ya tabbatar musu da cewa gwamnati ba za ta bari su wulaƙanta ba.

“Sojojinmu da suka rasa wasu sassa jikinsu ko suka samu raunuka ba za a bari a wulakanta su ba.

“Za mu ci gaba da tallafa musu domin sadaukarwarsu ba za ta tafi a banza ba,” in ji shi.

Ya jaddada cewa Najeriya ta cancanci girmamawa, kuma ba za ta yarda da rashin adalci daga kowace ƙasa ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jami’in tsaron al’umma 6 sun mutu a artabu da ’yan bindiga a Sakkwato
  • ’Yan bindiga sun Kashe mutum 2, sun sace manoma 10 a Neja
  • Hana Biza: Najeriya ta cancanci a girmama ta – Babban Hafsan Tsaro
  • Rigima ta sake kaurewa tsakanin PDP da APC a Zamfara
  • Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno
  • Kissoshin Rayuwa. Sirar Imam Alhassan (a) 19
  • An Gudanar Da Taron Bita Na Yini 4 Ga Malaman Tafsiri Da Ke Babura
  • Masu Alaka
  • Mutum biyu sun shiga hannu kan yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe a Yobe
  • Yadda na yi wa budurwar da muka haɗu a Facebook gunduwa-gunduwa —Matashi