Kwamfutar Quantum Ta Kasar Sin Ta Samu Masu Ziyara Sama Da Miliyan 20 Daga Sassan Duniya
Published: 16th, February 2025 GMT
Jaridar kimiyya da fasaha ta kasar Sin ta ba da rahoton cewa, kwamfutar da kasar Sin ta kera da kanta ta zamani na uku mai sarrafa bayanai tare da warware matsaloli cikin matukar sauri ko kwamfutar quantum a takaice, wato Origin Wukong, ta samu masu amfani da ita sama da miliyan 20 daga sassan duniya baki daya, wanda ya kasance wani muhimmin ci gaba a fannin bunkasa ayyukan da suka shafi kwamfutar quantum.
A cewar cibiyar nazarin injiniyan kwamfutar quantum ta Anhui, masu amfani daga kasashe ko yankuna 139 sun samu damar shiga Origin Wukong, tare da Amurka, Rasha, Japan da Kanada a matsayin mafi yawan yin amfani da ita. A cikin wadannan kasashe, Amurka ce ke kan gaba a ziyarar masu amfani daga kasashen waje. (Mohammed Yahaya)
এছাড়াও পড়ুন: