Kasar Sin Ta Kammala Gina Jirgin Ruwan FPSO Na Farko Na Duniya Mai Karfin Rikewa Da Adana Iskar Carbon
Published: 16th, February 2025 GMT
An kammala aikin gina wani jirgin ruwa sabon kira mai bambaro saman ruwa, da samarwa, da adanawa, da saukewa wato FPSO a takaice, wanda ke da na’urar rike iskar carbon da wurin adanawa, a Shanghai, a cewar Jaridar kimiyya da fasaha ta kasar Sin.
Jirgin dai shi ne irinsa na farko a duniya kuma ana shirin isar da shi a karshen watan Fabrairu, a cewar jaridar.
Jirgin na FPSO mai tsayin mita 333 da fadin mita 60, yana iya samar da danyen mai har ganga 120,000 a kowace rana. Kana yana iya aiki na musamman wajen rike iskar carbon dioxide da aka samar yayin kewayawa da ayyukan samar da mai. Bugu da kari, yana amfani da makamashin zafi daga iskar gas don samar da wutar lantarki, tare da cimma manufofi biyu na kare muhalli da tsimin makamashi, a cewar rahoton. (Mohammed Yahaya)
এছাড়াও পড়ুন: