Yadda Ake Magance Kumburin Idanu?
Published: 16th, February 2025 GMT
Shan ruwa hanya ce mafi sauwi wajen magance kumburin ido domin, ruwa yana wanke dauda a Ido. A samu cokulan karfe kamar biyar zuwa shida a saka a firiji na tsawon minti 10 zuwa 15 sannan a cire su, sai a rika shafawa a kumburin Ido har sai ido ya sabe.
Ganyen shayi yana magance kumburin Ido: A jika ganyen shayi a ruwan dumi, sannan a cire a bari ya huce.
A bari ya tsaya a hakan na tsawon minti biyar zuwa goma sannan a cire.
Wata hanyar magance kumburin ido ita ce: A samu gurji a yanka sannan a saka a firiji na tsawon minti goma sai a cire a dora a kan Idanuwan har sai sun huce.
এছাড়াও পড়ুন:
An wawushe motar abinci ta Hukumar WFP a Borno
Wasu da ba a san ko su wanene ba sun yi awan gaba da kayayyakin wata mota ɗauke da kayan abinci na Hukumar abinci ta duniya (WFP) a garin Gubio, yayin da take kan hanyarta ta zuwa Damasak a Jihar Borno.
Majiyar leƙen asiri ta shaidawa Zagazola Makama cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:30 na rana lokacin da Aminu Malam Umar direban wata babbar mota ƙirar Iɓeco ya tsaya a gefen titi.
’Yan adawa sun shirya ƙalubalantar Tinubu a zaɓen 2027 – Atiku Gobara ta ƙone gidaje tare da asarar dukiya a GombeYayin da motar ta tsaya a gefen titi ba tare da kula daga jami’an tsaro ba, wasu da ba a san ko su waye ba suka sace buhunan shinkafa da gishiri da sukari da wake da kuma man girki da dama, duk da cewa ba a tantance adadin da kuma darajar kayayyakin da aka sace ba har ya zuwa yanzu.
Jami’an tsaro sun ziyarci wurin da lamarin ya faru, amma ba a kama kowa ba.
Daga bisani sojoji sun ɗauke motar zuwa Gubio lafiya lau a yayin da ake ci gaba da bincike don gano waɗanda suka aikata laifin tare da ƙwato kayayyakin da aka sace.