Fusatattun matasa sun ƙone ofishin ’yan wanda a Ondo
Published: 17th, February 2025 GMT
Wasu fusatattun matasa sun banka wa ofishin ’yan sanda na yankin Ifon, da ke Ƙaramar Hukumar Ose wuta a Jihar Ondo.
Lamarin ya faru ne bayan da ake zargi ’yan sanda da azabtar da wani matashi har ya mutu a hannunsu.
An tsinci gawar ɗan sanda a Otal a Ogun NAFDAC ta gano wajen da ake sabunta magungunan da suka lalalce a AbiyaAna zargin al’amarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar, amma ba a samu cikakken bayani ba sai zuwa ranar Lahadi.
Wani mazaunin Ifon, wani gari da ke iyaka da Jihar Edo, ya shaida wa Aminiya cewa mutuwar matashin ta sa al’umma da abokansa yin bore.
Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne tun a ranar masoya.
Samun labarin mutuwar matashin ke da wuya, sai matasan suka ɗunguma zuwa ofishin ’yan sanda..
Ya ce ’yan sandan sun kasa shawo kan masu boren da suka mamaye ofishin, inda suka banka masa wuta a fusace.
Da ta ke tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta ce an tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin.
Ta kuma ƙara da cewa Kwamishinan ’yan sandan jihar, Wilfred Afolabi, na kan hanyarsa ta zuwa Ifon domin ta tabbatar da zaman lafiya da kuma hana sake aukuwar wani tashin hankali.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Edo ta tanadi hukuncin kisa kan masu garkuwa da mutane
A yunƙurin daƙile ta’adar garkuwa da mutane, Majalisar Dokokin Jihar Edo, ta amince da dokar zartar da hukuncin kisa kan duk wanda aka kama da laifin.
Majalisar ta amince da ƙudirin ne wanda ta yi wa bita daki-daki yayin zaman da ta gudanar a ranar Talata.
USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin AlbashiShugaban masu rinjaye na majalisar, Charity Aiguobarueghian ne ya jagoranci gabatar da ƙudirin wanda shugaban marasa rinjaye, Henry Okaka ya goyi baya.
A baya dai Majalisar Dokokin Edo ta ayyana hukuncin ɗaurin rai da rai ga duk wanda aka tabbatar wa laifin garkuwa da mutane tare da ƙwace duk wani abu da mallaka a dalilin aikata ta’adar ta garkuwa da neman kuɗin fansa.
Sai dai a yanzu majalisar dokoki ta sahale a tsananta matakin da za a riƙa ɗauka zuwa hukuncin kisa haɗi da ƙwace duk abin da aka mallaka ta hanyar aikata laifin.
Tuni dai Kakakin Majalisar, Blessing Agbebaku ya umarci Magatakardan majalisar da ya miƙa wa Gwamna Godwin Obasake ƙudirin domin amincewa.
Kazalika, majalisar ta amince da ƙudirin yi wa dokokin hukumomin samar da wutar lantarkin jihar gyaran fuska.