Fusatattun matasa sun ƙone ofishin ’yan sanda a Ondo
Published: 17th, February 2025 GMT
Wasu fusatattun matasa sun banka wa ofishin ’yan sanda na yankin Ifon, da ke Ƙaramar Hukumar Ose wuta a Jihar Ondo.
Lamarin ya faru ne bayan da ake zargi ’yan sanda da azabtar da wani matashi har ya mutu a hannunsu.
An tsinci gawar ɗan sanda a Otal a Ogun NAFDAC ta gano wajen da ake sabunta magungunan da suka lalalce a AbiyaAna zargin al’amarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar, amma ba a samu cikakken bayani ba sai zuwa ranar Lahadi.
Wani mazaunin Ifon, wani gari da ke iyaka da Jihar Edo, ya shaida wa Aminiya cewa mutuwar matashin ta sa al’umma da abokansa yin bore.
Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne tun a ranar masoya.
Samun labarin mutuwar matashin ke da wuya, sai matasan suka ɗunguma zuwa ofishin ’yan sanda..
Ya ce ’yan sandan sun kasa shawo kan masu boren da suka mamaye ofishin, inda suka banka masa wuta a fusace.
Da ta ke tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta ce an tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin.
Ta kuma ƙara da cewa Kwamishinan ’yan sandan jihar, Wilfred Afolabi, na kan hanyarsa ta zuwa Ifon domin ta tabbatar da zaman lafiya da kuma hana sake aukuwar wani tashin hankali.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An Bukaci Gwamnati A Kowani Mataki Da Ta Taimakawa Yaki Da Shan Magani Ba Bisa Ka’ida Ba
An yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su hada kai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar rage karuwar amfani da magungunan ba bias ka’ida ba a tsakanin matasa.
Babban Daraktan Kula da Lafiya (CMD,) a Babban Asibitin Neuro-Psychiatric na Tarayya, Budo Egba, Jihar Kwara, Dokta Issa Awoye, ya yi wannan kiran ne a cikin jawabinsa mai taken, Sakamakon Neuropsychiatric na Maganganun Magani: Ra’ayin Clinical a taron masu ruwa da tsaki na Kwara na biyu kan Kariya da Sarrafa miyagun kwayoyi, wanda aka gudanar a Ilorin.
A cewarsa an samu karuwar noma da fataucin miyagun kwayoyi a kasar, musamman a tsakanin matasa.
Ya jera magungunan da aka saba amfani da su sun hada da tramadol, codein maganin tari syrup, methamphetamine (meth), rohypnol, ecstasy da sauransu.
Dr.Awoye ya ce magungunan galibi suna da rahusa kuma sun fi amfani da su fiye da na gargajiya da ke haifar da babbar illa ga daidaikun mutane.
Ya bayyana cin hanci da rashawa da ke tsakanin jami’an tsaro da na hukumar a matsayin daya daga cikin kalubalen da ke kawo cikas ga kokarin dakile safarar miyagun kwayoyi a kasar.
A nasa jawabin, mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kwara kan yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, Mukail Aileru, ya ce gwamnatin jihar ta dukufa wajen ganin ta magance matsalar shan muggan kwayoyi.
Ya yi bayanin cewa karuwar tabarbarewar magungunan na haifar da babbar barazana ga lafiyar jama’a, tsaro, da makomar matasa”.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU