Sheik Na’im Kassim: Babu Dalilin Ci Gaba Da Zaman Sojojin Mamaya A Lebanon
Published: 17th, February 2025 GMT
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya gabatar da jawabi da marecen jiya Lahadi inda ya tabo muhimman batutuwa da su ka shafi kasar ta Lebanon da kuma yammacin Asiya.
Sheikh Na’im Kassim ya ce wajibi ne ‘yan sahayoniya su janye sojojinsu daga kudancin kasar ta Lebanon domin babu wani dalili na cigaba da zamansu.
Shekih Na’im Kassim ya bayyana ranar 23 ga watan nan na Febrairu ta jana’izar Shahid Sayyid Hassan da kuma shahid Hashim Safiyuddin a matsayin ranar jaddada mubaya’a ga tafarkin da ya tafiyar da rayuwarsa a kansa da shi ne gwgawarmaya.
Babban makatakardar kungiyar ta Hizbullah dai ya gabatar da jawabi ne na tunawa da jagororin Hizbullah da su ka gabata, inda ya yi kira da al’ummar kasar da su fito domin halartar jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah.
Sheikh Na’im Kassim ya ce; Ina yin kira ga al’ummarmu da su fito sosai domin halartar jana’izar shahidai, Sayyid Hassan Nasrallah da kuma Shahid Sayyid Hashim.”
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma bayyana cewa duk wanda yake son yin matsin lamba akan Hizbullah domin ya raunanata, to ya kwana da sanin cewa ba zai sami nasarar yin hakan ba.
Dangane da batun hana jirgin saman Iran sauka a filin saukar jiragen sama na Beirut, saboda barazanar HKI, babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kirayi gwamnatin kasar ta Lebanon da ta sauya matsayar da ta dauka.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Na im Kassim ya
এছাড়াও পড়ুন:
Fadar Mulkin Amurka: Tattaunawa Da Iran Ta Yi Armashi
Fadar mulkin Amurka ta “White Hosue” ta bayyana cewa tattaunawar da aka yi a tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci da wakilin Donald Trump akan gabas ta tsakiya Steve Witkoff, ta hanyar shiga tsakanin kasar Oman, ta yi armashi.
Da marecen jiya Steve Witkoff ya bayyana cewa; shugaba Donald Trump ya ba shi umarnin ya yi duk abinda zai iya domin rage tazarar sabanin da ake da ita ta hanyar tattaunawa da diflomasiyya.
Bayanin na fadar mulkin Amurka ya kuma yaba wa kasar Oman wacce ta kasance mai masaukin baki na tattaunawar da aka yi wacce ba ta gaba da gaba ba ce a tsakanin Amurkan da kuma Iran.
Gabanin bayanin na fadar mulkin Amurkan, manzon musamman na shugaba Donald Trump, Steve Witkoff ya fada wa tashar talabijin din NBC cewa, ya yi tattaunawa mai matukar armashi da kuma amfani.
Tun a ranar Asabar da safe ne dai ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci ya isa birnin Mascut, inda ya gana da takwaransa na kasar Sayyid Hamad Bin Hamud al-Busa’idi, tare da mika masa bayanai da su ka kunshi mahangar Iran akan tattaunawar.
Ministan na harkokin wajen Oman ya zama mai shiga tsakanin kasashen biyu a tsawon lokacin tattaunawar. Bangarorin biyu sun yi musayar takardu har sau hudu.
A ranar Asabar mai zuwa ne dai za a ci gaba da tattaunawar daga inda aka tsaya a wani wurin da ba a kai ga ayyana shi ba.