DRC: An Shiga Damuwa A Birnin Bukavu Da ‘Yan Tawaye Su Ka Kwace Iko Da Filin Saukar Jiragen Sama
Published: 17th, February 2025 GMT
Rahotanni da suke fitowa daga Bukavu sun ambaci cewa ‘yan tawayen kungiyoyin M 23 da kuma AFC sun kwace iko da filin sauran jiragen sama na Kavumu wanda yake da tazarar kilo mita 45 daga birnin.
mutanen sun kauracewa zirga-zirga akan titunan birninna Bukavu saboda rashin tabbacin abinda zai biyo baya.
Mafi yawancin ‘yan siyasa a birnin sun buya,saboda karatowar ‘yan tawayen cikin birnin.
Wasu rahotannin suna nuni da cewa, ‘yan tawayen sun shiga cikin birnin na Bkavu, a jiya Lahadi.
Bukavu dai shi ne birni na biyu da ‘yan tawayen su ka kama daga farkon watan Janairu zuwa yanzu, bayan da su ka shiga cikin birnin Goma.
An Shiga Rudani A Birnin Bukavu .
Sojojin DRC da kawayensu na kasar Burundi sun janye daga cikin barikokin birnin tun a ranar Juma’a da ita ce ranar da ‘yan tawayen su ka kwace iko da filin saukar jiragen sama.
An rika jin karar bindiga da ake harbe-harbe a cikin birnin da kuma wawason da ake yi a dakunan ajiya na hukumar abinci ta duniya ( WFP).
Kustawar da kungiyoyin ‘yan tawayen suke yi a cikin biranen DRC, yana haddasa fargaba akan yiyuwar barkewar yaki a cikin yakin. Kungiyar M 23 dai tana samun goyon bayan ne daga kasar Rwanda yayin da ita gwamnatin kasar DRC take da nata kawayen a cikin yankin da su ka hada da Brundi. MDD dai ta sha yin kira da a tsagaita wutar yaki da kawo karshe fadace-fadacen da ake yi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Yaya ‘Yan Siyasar Amurka Ke Kasafta Harajin Ramuwar Gayya?
Manufar “ramuwar gayya” ba za ta daidaita gibin cinikin da kasar Amurka take fuskanta ba, illa ta daga farashin kayan da ake shigarwa kasar daga kasashen waje, da haddasa hadarin hauhawar farashin kaya a kasar, da kawo illa ga zaman rayuwar jama’ar kasar. A karshe Amurka ba za ta cimma burinta na zama a matsayin koli a duniya ba. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp