Malaman addini sun yi wa ’yan siyasa juyin mulki —Sule Lamiɗo
Published: 17th, February 2025 GMT
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamiɗo, ya zargi malaman addini da neman ƙwace lamurran siyasar Najeriya daga hannun ’yan siyasa.
Sule Lamiɗo ya nuna damuwa bisa yadda malaman addini ke ƙara shiga harkokin siyasa, inda ya ce, a halin yanzu malaman suna yin tasiri sosai a yanayin tafiyar siyasa da kuma jefa ƙuri’a.
Ya bayyana haka ne a yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikum, bisa rasuwar babban ɗansa a Jihar Kaduna.
A cikin bidiyon ta’aziyyar, an ji Sule Lamiɗo, yana cewa, malaman addini sun yi wa ’yan siyasa ƙwace, inda suke fitowa fili suna yi wa ’yan takara yaƙin neman zaɓe, tare da kiran mabiyansu su zaɓi wanda su suke goyon baya.
Tsohon Ministan Harkokin Wajen na Najeriya ya ce, “duk da ni’imar da Allah Ya yi musu na kasancewa malaman addini, amma yanzu sun koma yin kokawa da ’yan siyasa.
“Kamata ya yi malaman addini su zama iyaye masu shiryatar da al’umma, amma tunda mulki suke so, to mun ’yan siyasa za mu bar musu, mu koma gefe.”
Cikin shaguɓe ya ci gaba da cewa, “muna jira su fito su gaya mana wanda suke so mu zaɓa gwargwadon abin da suke so.” Sannan ya ce, “Idan har ana so a samu adalci da daidaito a Najeriya, to dole sai kowa ya tsaya a matsayinsa a cikin al’umma.”
Jigon Jam’iyyar adawa ta PDP, ya bayyana cewa an wayi gari rikicin cikin gida da rarrabuwar kai sun dabaibaye ƙungiyoyin da ɗarikun addini, kamar yadda jam’iyyun siyasa ke fama da waɗannan matsaloli.
Daga nan sai ya ce muddin ba a samu haɗin kai ba, tsarin siyasar Najeriya ba zai taɓa rabuwa da rikici ba.
Tasirin malamai a siyasar NajeriyaA baya malaman addini sun yi tasiri matuƙa wajen sanya magoya bayansu su yi rajistar zaɓe.
Amma a zaɓen 2023, wanda ake wa kallon rarrabuwar kai ta dabaibaye fiye da kowanne, malaman sun zarce hakan, inda suka riƙa bayyana ’yan takarar da suke goyon bayan.
Lamarin ya kai ga wasu malaman suna fitowa a huɗubobinsu, suna bayyana ɗan takarar da suke goyon baya a cikin ’yan takara.
Wasu malaman Musulunci sun rika shawarar mabiyansu da su kaɗa kuri’a bisa la’akari da addinin ’yan takara. A ɗaya ɓangaren kuma, malaman Kirista sun riƙa iƙirarin samun ilhama gane da ɗan takarar da zai lashe zaɓen na 2023. Sai dai kuma mafi yawan waɗannan iƙirarin ba su abbata da.
Dambarwar malaman addiniKo a baya-bayan nan, taƙaddama ta ɓarke tsakanin malaman Musulunci kan taron Mahaddata Al-Ƙur’ani da aka shirya gudanarwa a Abuja ranar 22 ga watan nan na Fabrairu, 2025, inda ake sa ran tara Mahaddata da Masu Zayyana da makaranta Al-Kur’ani mutum 30,000.
An ɗage taron zuwa abin da hali ya yi damuwar da wasu malaman Musulunci suka nuna kan halascin taron da kuma zargin cewa yana da alaƙa da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Takarar Muslim-MuslimIdan ba a manta ba dambarwar zaɓen Musulmi da Musulmi a lokacin takarar Shugaba Bola da mataimakinsa Kashim Shettima ya tayar da ƙura a fagen siyasar Najeriya a kakar zaɓen 2023.
Amma dai ’yan takarar sun kai labari a zaɓen saboda gagarumar goyon bayan da wasu malamai suka ba shi, suka kuma kwaɗaita wa mabiyansu alherin da ke tattare da hakan.
Bambancin addini da kabilanci sun kuma yi tasiri a yankin Kudu maso Yamma a kakar zaɓen.
A yankin Arewa muƙarraban Tinubu sun nema kuma sun samu goyon bayan manyan malaman addini wajen tallata shi. Da alama kuma irin haka ta sake kunno Kai, duba da yadda manyan ’yan siyasa suka fara shirye-shiryen zaben 2027.
Sai dai kuma akwai alama tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar LP, Mista Peter Obi, ya far sauya taku, inda a wannan karon yake ƙara matsa ƙaimi domin samun gagarumar goyon baya a yankin Arewa, inda Musulmi suka fi rinjaye.
Ana ganin halartarsa tarukan buɗa-baki a lokacin azumin watan Ramadan da kuma shigarsa harkokin da suka shafa al’ummar da kuma bayar da gudunmawar kuɗaɗe a matsayin wani salo na zawarcin al’ummar yankin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Najeriya Siyasa Takara siyasar Najeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Hajji 2025: Kamfanin Saudiyya zai maka Najeriya a Kotun Duniya
Kula da walwalar maniyyatan Najeriya ya shiga tangal-tangal bayan wani kamfanin kula da alhazai na kasar Saudiyya ya yi barazanar maka Najeriya a Kotun Hukunta Manyan Laifuka na Duniya (ICC), kan saba yarjejeniyar kwangilar aikin Hajji.
Kamfanin Mashariq Al Dhahabiah Al Mutawazi na kasar Saudiyya, wanda Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) da Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohin suka ba wa kwangilar kula da alhazan Najeriya a aikin Hajjin 2025, ne ya yi barazanar, yana mai zargin Najeriya da yaudarar sa.
Mashariq Al Dhahabiah Al-Mutawazi ya yi barazanar maka Najeriya a Kotun Duniya ne bisa zargin Hukumar NAHCON da karya yarjejeniyar da suka kulla kan aikin kula a alhazan, musamman a Mina da Filin Arfa.
A wata wasika da ya aike wa Shugaban Ofishin Aikin Hajjin Najeriya da ke birnin Makkah a kasar Saudiyya a ranar Litinin 17 ga watan nan na Fabrairu, 2025, kamfanin ya zargi NAHCON da saba yarjejeniyar da suka kulla cewa kanfaninsu ne kadai hukumar za ta wa kwangilar aikin a bana, musammana a Mina da Arafah.
NAJERIYA A YAU: Ci-gaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Za Su Samar Dattijon Neja Delta Edwin Clark ya rasuDaga nan sai ya ba wa hukumar kwana 20 ya koma kan sharudan yarjejeniyar da suka rattaba hannu a kai, idan ba haka ba ta maka hukumar a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC).
Binciken wakilinmu ya gano a ranar 17 ga watan Janairu ne kamfanin da NAHCON suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kula da alhazan Najeriya a Kasa Mai Tsarki.
Amam daga bisani Kungiyar Hukumomin Jin Dadin Alhazan Jihoi suka daga kara cewa Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman Saleh, ya yi gaban kansa wajen soke yarjejeniyar, kwanaki kadan kafin cikar wa’adin biyan kudi ga kamfanonin da kasashe suka ba wa aikin.
Farfesa Abdullahi Usman Saleh dai ya musanta yin gaban kansa wajen soke yarjejeniyar, yana mai cewa hukumomin Saudiyya ne suka yi.
Ana zargin NAHCON ta raba aikin gida biyu tsakanin Mashariq Al Dhahabiah Al Mutawazi da kuma kamfanin Ikram Diyafa kafin cikar wa’adin ranar 14 ga watan Janairu da hukumomin Saudiyya suka sanya.
Mashariq Al Dhahabiah Al Mutawazi na zargin NAHCON da ba shi aikin kula da alhazai 26,287, duk kuwa da cewa hukumar ta sanar cewa ta samu tantunan alhazai 52,544 da za su gudanar da aikin Hajjin, wanda hakan ke nufin hukumar ta ba wa daya kamfanin aikin kula da ragowar alhazai 26,257 ke nan.
Kamfanin ya bukaci zama na gaggawa da mahukuntan NAHCON kan lamarin domin yanke shawara kan mataki na gaba da za a dauka.
Wakilinmu ya yi iya kokarinsa domin samun martanin hukumar NAHCON a game da wannan dambarwa, amma abin ya faskara.