Leadership News Hausa:
2025-04-14@17:58:36 GMT

Shugaban Pakistan: Ci Gaban Kasar Sin Al’amari Ne Mai Kyau

Published: 17th, February 2025 GMT

Shugaban Pakistan: Ci Gaban Kasar Sin Al’amari Ne Mai Kyau

Wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin ta yi hira da shugaban Pakistan, Asif Ali Zardari, dake ziyarar aiki a kasar Sin, a baya bayan nan a birnin Beijing. Yayin hirar, Zardari ya bayyana cewa, ci gaban kasar Sin al’amari ne mai kyau, kuma Sin ba ta taba zama mai mamaya ba.

Bisa ci gaban Sin cikin sauri, wasu kasashe suna daukarta a matsayin wata “barazana”.

Game da hakan, Zardari ya ce, a matsayin makwabciyar kasar Sin, kasar Pakistan ta san a ko da yaushe Sin ba ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe, kila ne a ji tsoron sauran kasashen duniya, amma ba kasar Sin ba. (Safiyah Ma)

 

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Jiragen Yakin Kasar Amurka Suna Rusa Cibiyoyin Ilmi A Hare-Haren Da Suke Kaiwa Kasar Yemen

Jiragen yakin Amurka sun kai sabbin hare-hare kan wasu yankunan a kasar Yemen a safiyar a jiya Asabar, wadanda suka Baida Sa’ada da kuma Hudaidah wadanda sune sake zafafa yaki a ciki kasar na baya-bayan nan.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labarai na kasar ta Yemen na fadar cewa jiragen yakin kasar ta Amurka sun kai  hare-hare har 5 a kan makarantar koyon sana’o’ii na Al-sawma  da ke lardin  Al-Bayda a jiya Asabar .

Labarin ya kara da cewa makarantar ita ce babbar makaranta a yankin, kuma cibiyar ilmi mafi girma. Har’ila yau labarin ya bayyana cewa jiragen yakin kasar ta Am,urka sun kai hare-hare har guda 3 a kan garin Al-Sahleen daga cikin yankunan Kitif da kuma Al-Bogee daga cikin lardin Sa’ada.

Labarin ya kara da cewa wannan yankin yana daga cikin yankunan da ake fafatawa da sojojin  Amurka, kuma suna yawaita kan hare-hare a cikinsa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yar shekara 66 ta haifi ɗanta na 10 da kanta
  • Shugaban Kasar Iran Ya Mika Ta’aziyyar Ta Rasuwar Wanda Ya Assasa Hukumar  Makamashin Nukiliya Ta Iran
  • A Kasar Gabon Brice Oligui Nguema Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa
  • Brice Ologui Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Gaban Da Kashi 90.35% A Jiya Lahadi
  • Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Makiya Suna Hasadan Ci Gaban Kasar Iran
  • Dagewa Iran Takunkuman Zalunci Na Daga Cikin Manufofin Tattaunawa Da Amurka: Aref
  • Ukraine na Fuskantar Wata Barazana, Dangane Da Bukatar Amurka Na Kwace Iko Da Cibiyar Gas Na Rasha  A cikin Kasar
  • Jiragen Yakin Kasar Amurka Suna Rusa Cibiyoyin Ilmi A Hare-Haren Da Suke Kaiwa Kasar Yemen
  • Jama’ar Gabon sun kada kuri’a a zaben shugaban kasa, na farko bayan mulkin zuri’ar Bongo
  • Shugaban Hukumar Makamashin Nukliya Ta Kasar Iran Ya Ce Dukka Ayyukan Makamashin Nukliya A Cikin Gida Suna Tafiya Da Karfinsu