Ƴan Nijeriya 85 Za Su Iso Lagos Daga Amurka A Yau
Published: 17th, February 2025 GMT
Gwamnatin Amurka ta fara aiwatar da matakan korar ‘yan Nijeriya daga ƙasar, inda ake sa ran mutane 85 za su iso Lagos, yayin da wasu 116 ke tsare.
Jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills, ya bayyana haka yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Ministan harkokin wajen Nijeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, a Tafawa Balewa House da ke Abuja.
A nata ɓangaren, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu ta bayyana damuwa kan yadda ake gudanar da tsare-tsaren korar mutanen, inda ta buƙaci da a bi ƙa’idojin da suka dace na ƙasa da ƙasa. Ta jaddada cewa dole ne a samar da hanyoyin da za su rage raɗaɗin korar, musamman ga waɗanda ba su aikata wani laifi na tashin hankali ba.
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Irin Gagarumar Rawar Da Iran Ta Taka A Fegen Tsaro Yakin Tekun Pasha
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Iran tana taka rawa ta musamman wajen wanzar da kwanciyar hankali da tsaron yankin Tekun Pasha
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta hanyar mallakar mafi yawan layukan kan iyaka da tekun Pasha da kuma iko da mashigar Hormuz, ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali da tsaron wannan ruwa da yankunan makwabtanta.
Abbas Araqchi ya bayyana hakan ne a yayin taron tarihin huldar kasashen waje na Iran karo na 8, mai taken “Manufar harkokin wajen Iran da gabar tekun Pasha a cikin mahallin tarihi,” wanda aka gudanar a safiyar yau Talata a cibiyar nazarin siyasa da kasa da kasa na ma’aikatar harkokin wajen kasar: Tun daga tsawon tarihi har zuwa yanzu, yankin Tekun Pasha, yana matsayin daya daga cikin muhimman bangarorin ruwa a duniya, kuma yana daya daga cikin muhimman yankuna da suka shafi ci gaban rayuwar bil’adama, da muhimman tsare-tsare a fuskar mahanga daban-daban na bangarorin rayuwar dan Adam, wannan yanki na tekun Pasha yana nan a tunanin bil-Adama kuma ya cancanci matsayi da kulawa da bincike daga bangarori daban-daban.