Kotu Ta Hana Gwamnatin Tarayya Riƙe Wa Kano Kuɗaɗen Ƙananan Hukumomi
Published: 17th, February 2025 GMT
“Hakkinmu ne mu tabbatar da cewa kuɗin jama’a ba su faɗa hannun jagorori marasa cancanta ba. Saboda haka, za mu ɗaukaka ƙara kuma mu ci gaba da fafutuka har sai an yi mana adalci,”
in ji shi.
.এছাড়াও পড়ুন:
Za a hukunta ma’auratan da suka ci zarafin yarinya a kan mangwaro — Zulum
Gwamnatin Jihar Borno, ta ɗauki matakin hukunta wasu ma’aurata, Mamman Sheriff da matarsa, da aka kama suna cin zarafin wata yarinya a unguwar Pompomari Bypass da ke Maiduguri.
Bayan bayyanar faifan bidiyon da ya nuna ma’auratan suna dukan yarinyar, mutane da dama sun yi tir da abin a shafukan sada zumunta.
Majalisar Wakilai ta musanta karɓar kuɗi kan dokar ta-ɓaci a Ribas Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar NamibiaWannan ya sa Hukumar Tsaron Sibil Difens (NSCDC) ta cafke su nan take.
Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da cewa gwamnati ba za ta musu sassauci ba.
Ya ce ma’aikatun shari’a, ilimi, da harkokin mata sun haɗa kai domin ganin an hukunta waɗanda suka aikata laifi.
Yarinyar, wacce ɗaliba ce, ta shiga harabar gidan ma’auratan domin tsinkar mangwaro bayan tashi daga makaranta, inda suka yi mata dukan kawo wuƙa.
A halin yanzu tana kwance a asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH), inda Dokta Lawan Bukar Alhaji ya ɗauki nauyin jinyarta.
Gwamnatin Borno ta kuma tallafa wa iyayen yarinyar da kayan agaji, abinci, da kuɗi.
Iyayenta da sauran jama’a sun yaba wa gwamnatin kan matakin da ta ɗauka na kare haƙƙin yarinyar.
Gwamnati ta jaddada cewa duk wanda aka kama da cin zarafin yara ba zai tsira daga hukunci ba.