Trump Ya fadawa Turawa Kan Cewa Basa Cikin Tattaunawa Kan Tsagaita Wuta A Ukraine
Published: 17th, February 2025 GMT
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa kasashen Turai basa cikin tattaunawar tsagaita wuta a Ukraine. Jaridar Daily Mail ya bayyana cewa hankalin shuwagabannin kasashen turai ya tashi a lokacin da JD Vance mataimakin shugaba Trump ya fada masu cewa ba wani shugaba daga cikin shuwagabannin kasashen Turai da zasu halarci taron tsagaita wuta na Ukraine.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar OCHA Ta Bayyana Cewa Yahudawan Sahyoniyya Sun Ninninka Ayyukan Korar Falasdinawa A Yamma Da Kogin Jordan
Hukumar kula da agaji ta MDD (OCHA) ta bada sanarwan cewa, gwamnatin HKI a yankin yamma da kogin Jordan ta kori Falasdinawa a gidaje 5 a yankin bayan sun rusa gidajensu. Hukumar ta kara da cewa wadanda HKI ta rusa gidajensu a yankin sun hada da yara 19 da da iyayensu 33 maza da mata 6.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto OCHA na cewa tun watan Maris da ya gabata zuwa yanzu, HKI ta rusa gidaje da gine-ginen Fafalsadinawa kimani 100 a yankin yamma da kogin Jordan wadanda suka hada da gabacin birnin Qudus da kuma sauran yankuna, da sunan an gina gidajen ba bisa ka’ida ba.
Banda haka suna kwace gonakin Falasdinawa don ginawa sabin yahudawan da suke shigowa kasar matsugunai.
Labarin y ace, a wasu lokutan yahudawan zasu tilastawa Falasdinawa rusa gidajensu da kansu ko kuma idan sun rusa su da kayan aikinsu su tilastawa Falasdinawan kbiyan kudaden aikin rusawan.