Kungiyoyin Hamas Da Jihadul Islami Da Hamas Sun Yi Tirsa Da HKI Kan Azabtar Da Falasdinawa A Gidan Yarin Ofer
Published: 17th, February 2025 GMT
Kungiyoyin Hamas, Jihad Isalami da kuma sauransu a kasar Falasdinu da aka mamaye sun bayyana yi allawadi da HKI saboda yadda suke zazabtar da fursinonin Falasdinawa a gidan yarin Ofer, kamar yadda labari ya ke isa daga ca.
Tashar talabijin ta Presstv na takalto cewa gidan yarin ofer ya na yammacin birnin Ramallah, a yankin yamma da kogin Jordan.
Kungiyoyin sun bayyana cewa, wannan shi ne halin ta’addanci da kuma kekacewar zuciya yahudawan sahyoniyya.
Daga karshe kungiyoyun sun yi kara da wadanda abin ya shafa su rika sanya ido sannan su aikata abinda ya dace don kawo karshen wahalar falasdinawa a gidajen yarin Ofer.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Dubban Falasdinawa Sun Kauracewa Gidajensu A Dai-Dai Lokacinta Sojojin HKI Suke Fafatawa Da Dakarun Falasdinawa
Dubban Falasdinawa ne suka kauracewa gidajensu a yankin yamma da kogin Jordan. Tun ranar 21 ga watan Jeneru na wannan shekara ta 2025, wato kwanaki biyu kacal da tsaida wuta a Gaza, sojojin HKI suka fadawa sansanin yan gudun hijira na Jenen inda suka fara fafatawa da dakarun Falasdinawa a yankin. Da nufin korarsu.
Dagan nan ne dubban Falasdinawa suka fara kauracewa gidajensu a yankin. Wasu suka dauki dukkan iyalansu su a mota su tafi inda ba’a tashin hankali. Wasu kuma sukan taka da kafafuwansu zuwa nesa daga inda ake fada da tashin hankali.
Wani dan agaji a yankin ya bayyana wa Jaridar ‘Arabsnews’ cewa bai taba ganin irin wannan kaurar da Falasdinawa suke yi ba, sai wanda aka yi a yakin 1967 inda falasdinawa 300,000 suka kauracewa gidajensu, sai kuma kafin haka a shekara ta 1948 falasdinawa 700,000 ne, sojojin yahudawan suka tilastawa falasdinawa kauracewa yankunansu a kasarsu da aka mamaye.