HKI Ba Zata Yarda A Kafa Kasar Palasdinu Ba, Saboda Barazana Ce Ga Wanzuwar HKI
Published: 17th, February 2025 GMT
Ministan tsaron HKI Israel Katz ya bayyana cewa gwamnatin HKIba zata bar a kafa kasar Falasdinu ba, saboda hakan barazana ce ga samuwar HKI.
Israek Kazt ya bayyana haka ne a lokacin ganawar jami’an gwamnatin HKI da tawagar kasar Amurka.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a taron su da tawagar kasar ta Amurka a yau.
Wasu kafafen yada labarai sun nakalto wasu manya manyan jami’an sojojin kasar suna tunanin dakatar da tsagaita wuta da suka kulla da Hamas. Banda haka suna ganin shawarar shugaba kasar Amurka Donal Trump n araba gaza da Falasdinawa ne kawai zai tabbatar da wanzuwar HKI.
Kafin haka dai Banyamin Natanyahu ya fadawa kafafen yada labarai kan cewa Falasdinawa suna da damar su bar Gaza su je inda suka ga dama, idan sun bukaci hakan, amma idan bas u yi ba, to mai yuwa a kashesu gaba daya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Mayar Da Martani Ga Tattaunawar Amurka Da Rasha Kan Rikicin Ukraine
Kasar Sin na maraba da duk kokarin da ake yi cikin lumana don warware rikicin kasar Ukraine, ciki har da tattaunawa tsakanin Amurka da Rasha, kuma Sin na fatan dukkan bangarori da masu ruwa da tsaki za su shiga cikin shawarwarin samar da zaman lafiya in lokaci yayi.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na yau Talata, yana mai cewa, ko da yaushe kasar Sin tana da yakinin cewa, tattaunawa da yin shawarwari, ita ce hanya daya tilo da za a iya warware rikicin, kuma ta himmatu wajen inganta shawarwari don samar da zaman lafiya.
Ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga wata tambaya game da ganawar da jami’an Amurka da na Rasha suka yi a ranar Talata a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, ba tare da halartar Ukraine ba. (Mohammed Yahaya)