Gwamnati ta raba wa mata tallafin awakai na N5bn a Katsina
Published: 17th, February 2025 GMT
Gwamnatin Katsina ta kashe kimanin Naira biliyan 5.4 domin bai wa mata 3,610 tallafin kiwon awakai.
Gwamna Dikko Umar Radda ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da shirin raba tallafin awakan a gundumar Dan-Nakolo da ke Ƙaramar Hukumar Daura ta jihar.
Gwamnati ta kashe N5bn domin bai wa mata tallafin kiwon awakai a Katsina NAJERIYA A YAU: Dalilan Saukar Farashin Kayan Masarufi A KaswanniYa bayyana cewa, a ƙarƙashin shirin, an raba wa mata 3,610 awakai huɗu-huɗu a gundumomi 361 da ke faɗin jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa wannan shiri wani ginishiki ne na bunƙasa harkokin noma da kiwo wanda yake da burin ganin Katsina ta zama ja gaba a fannin dogaro da kai a Arewacin Nijeriya da ma ƙasar baki ɗaya.
A cewar Gwamnan, kiwon awakai yana da muhimmanci kuma ɗaya ne daga cikin muradin gwamnantinsa na bunƙasa harkokin noma da kiwo da wadatar abinci sannan kuma abin dogaro da kai ga ƙananan manoma.
A nasa jawabin, mashawarcin gwamnan ma musamman kan harkokin kiwo, Suleiman Yusuf, ya ce bai wa mata tallafin awakai babbar hujja kan yadda gwamnatin ke ƙoƙarin ganin ta rage talauci a tsakanin al’umma.
“Mun ƙaddamar da wannan shiri ne saboda fahimtar da muka yi wa muhimmacin da rawar da mata suke takawa wajen bunƙasar tattalin arziki.
“Saboda haka wannan tallafi aka bai wa matan muna da yaƙinin cewa zai kawo kyakkyawan sauyi a tsakanin al’umma,” in ji Yusuf.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Katsina bai wa mata
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnati ta kama mutum 347 kan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba
Gwamnatin Tarayya ta kama mutum 347 da ake zargi da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a sassa daban-daban na Najeriya, inda aka gurfanar 143 a kotu.
Kama mutanen ya biyo bayan kafa wata runduna a shekarar 2024 don daƙile ayyukan haƙar ma’adanai ba ƙa’ida ba.
Kotun ƙoli ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren PDP Kwankwaso ya yi Allah-wadai da ayyana dokar ta-ɓaci a RibasMinistan Ma’adanai, Dele Alake, ya ce gwamnati na ƙoƙarin tabbatar da an hukunta mutum 327 da ke gaban kotu.
“A wannan watan, Babbar Kotun Tarayya da ke Ilorin ta yanke wa wasu ‘yan kasashen waje guda biyu, Yang Chao da Wu Shan Chuan, hukuncin ɗaurin gidan yari kan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.
“Muna jinjina wa EFCC saboda ƙoƙarinta na gurfanar da masu aikata laifin,” in ji Alake.
Ministan ya ƙara da cewa runduna da aka kafa ta ƙwato wuraren haƙar ma’adanai guda 98, kuma ta gano wasu haramtattun wurare guda 457.
Gwamnati na shirin faɗaɗa ayyukan rundunar zuwa wasu jihohi tare da amfani da fasaha kamar jiragen sama marasa matuƙa da sauran na’urori don sanya ido.
“Rundunar ta ƙwace wuraren da wasu suka mamaye sama da shekaru 10 ba bisa doka ba.
“Wannan zai taimaka wajen bunƙasa kuɗaɗen shiga daga ɓangaren ma’adanai,” in ji shi.
Ministan ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ƙara yawan jami’an tsaro da kayan aiki domin daƙile ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.
Ya gargaɗi duk masu aikata irin waɗannan laifuka da su daina, ko kuma su fuskanci hukunci.