Mutum biyu sun shiga hannu kan yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe a Yobe
Published: 17th, February 2025 GMT
’Yan sanda sun yi nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargi da laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 12 fyaɗe a kauyen Jalingo da ke Ƙaramar Hukumar Tarmuwa a Jihar Yobe.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya fitar a Damaturu ranar Litinin.
Ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:30 na yammacin ranar 15 ga watan Fabrairu, inda waɗanda ake zargin suka kai yarinyar wani kango a jeji suka keta mata haddi.
Rahoton na cewar, “Hedikwatar ‘yan sandan jihar reshen Ƙaramar Hukumar Tarmuwa ta cafke waɗanda ake zargin da suka haɗa baki tare da yi wa yarinyar ‘yar shekara 12 fyade, inda suka ji mata munanan raunuka.”
“Kamar yadda majiyar ke nunawa tuni wannan yarinya ta samu kulawa cikin gaggawa, yayin da aka miƙa waɗanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jiha (SCID) da ke Damaturu domin gudanar da bincike mai zurfi akan su,” in ji Abdulkarim.
Haka nan a wani samame da aka yi, kakakin ya ce an kuma kama wasu ɓata gari uku a unguwar Alimari da ke Damaturu bisa zargin ɗauke wani babur tare da lalata shi kwanan nan a unguwar Abbari da ke cikin birnin na Damaturu.
A cewarsa, waɗanda ake zargin sun ɓoye babur ɗin ne da wasu kayayyaki a wani gini da ba a kammala ba a yankin.
Ya ce jami’an nasu da ke aiki a ofishin ‘yan sanda na A Divisional, sun kai farmaki gidan tare da cafke waɗanda ake zargi da aikata laifin satar babur ɗin.
Har ila yau, SP Abdulkarim ya ce hedikwatar ‘yan sanda ta Gujba tare da haɗin gwiwar ‘yan banga sun ceto wani matashi daga hannun masu garkuwa da mutane a ƙauyen Daddawel.
Ya ce matashin da aka yi garkuwa da shi a ranar 12 ga watan Fabrairu, ya shakami iskar ’yanci ne bayan wani artabu tsakanin masu garkuwar da ‘yan sanda da ‘yan sa kai, lamarin da ya tilasta wa masu laifin gudu suka bar wanda aka yi garkuwar da sauran kayayyaki ciki har da wata bindiga guda ɗaya.
Abdulkarim ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Garba Ahmed, ya yaba da ƙoƙarin jami’an rundunar, inda ya ba da tabbacin ɗorewar yaƙi da miyagun laifuka a jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: fyaɗe Jihar Yobe yarinya waɗanda ake zargin
এছাড়াও পড়ুন:
Mutum 10 sun rasu, an lalata dukiyar N11bn yayin zanga-zangar yunwa a Kano — Rahoto
Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka.
Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na ’yan kasuwa a faɗin jihar.
Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko HaramDa yake jawabi a taron majalisar zartaswar ta jihar karo na 25 a ranar Talata, Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton daga shugaban hannun kwamitin, Mai shari’a Lawan Wada (ritaya).
Ya tabbatar da cewa za a fitar da takarda a hukumanci don bayyana waɗanda suka ɗauki nauyin tashin hankali yayin zanga-zangar.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bsture Dawaki Tofa ya fitar, zanga-zangar ta yi sanadin rasuwar rayukan mutum 10, yayin da wasu bakwai duka samu munanan raunuka.
Hakazalika ya ce an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11.
“Na gamsu da gaskiya da ƙwarewar mambobin kwamitin. An zaɓe su bisa cancanta, kuma ina da yaƙinin sun yi aikinsu ba tare da son rai ba,” in ji Gwamna Abba.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa ba ta tsoma baki a binciken da ya ɗauki watanni shida ana yi ba, domin bai wa kwamitin damar gudanar da aikinsa yadda ya kamata.
“Gwamnati za ta ɗauki matakin da ya dace dangane da abubuwan da aka gano a cikin rahoton.
“Wannan zai zama izina ga masu tayar da tarzoma da haddasa ɓarna a jihar,” a cewarsa.
Da yake gabatar da rahoton, Mai shari’a Wada, ya bayyana cewa kwamitin ya ziyarci wuraren da abin ya shafa tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin tattara bayanai kan tasirin zanga-zangar.
“Alƙawarin da gwamnan ya ɗauka na aiwatar da shawarwarin rahoton yana nuna matakin da za a ɗauka don tabbatar da adalci da daidaito a Jihar Kano,” in ji sanarwar.
Gwamna Abba ya yaba wa kwamitin bisa aikin da suka yi, kuma ya buƙace su da su kasance a shirye idan gwamnati ta sake neman su za su yi wani aiki.