Kungiyar M23 Ta Kwace Wani Birni Na Biyu A Gabashin DR Congo
Rahotanni daga Congo na cewa Kungiyar yan tawayen DR Congo ta M23 ta kutsa birnin Bukavu birnin mafi girma a gabashin kasar, inda ta kwace ofishin gwamnan lardin.
Bayanai sun ce mayakan sun kutsa cikin birnin ba tare da fuskantar wata tirjiya ba, kuma sun samu tarba mai kayu daga jama’ar yankin.
Bukavu shi ne birni na biyu mafi girma a yankin da ƴan tawayen suka karbe bayan Goma mai kunshe da albarkatun kasa.
A ranar Juma’a ne mayakan suka kame filin jirgin saman birnin na Bukavu da ke da tazarar kilomita 30 arewa da birnin – daga nan kuma sai suka nufi birnin wanda shi ne babban birnin lardin Kudancin Kivu.
Gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo (DRC), ta yi Allah wadai da shigar kungiyar ‘yan tawaye ta M23 cikin Bukavu, inda ‘yan tawayen sun kwace iko da muhimman wurare da dama.
Cikin wata sanarwa, gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta tabbatarwa al’umma cewa tana bibiyar yanayin da ake ciki a Bukavu, hedkwatar lardin Kivu ta kudu, inda ‘yan tawayen suka shiga.
Gwamnatin dai ta nanata kudurinta na tabbatar da oda da tsaro da cikakken ikonta, tana mai kira ga mazauna Bukavu su zauna a gida.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kwana Daya Bayan Kwace Fadar Shugaban Kasa, Sojojin Sudan Sun Kwace Babban Bankin Kasar
A ci gaba da shimfida ikonsu da suke yi a cikin birnin Khartum, sojojin Sudan sun kwace iko da babban bankin kasar, kwana daya bayan da su ka kori dakarun kai daukin gaggawa daga fadar shugaban kasa.
Kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya nakalto majiyar sojojin Sudan tana cewa; A yau Asabar sun yi nasarar kwace iko da babban bankin kasar, tare kuma da shimfida ikonsu a cikin wasu yankunan na birnin Khartum.
Kakakin sojan kasar Sudan Nabil Abdullah, ya bayyana cewa; Mun rusa sojoji da kayan aikin abokan gaba. Haka nan kuma Abdullah ya sanar da kwace wasu ma’aikatu da suke a tsakiyar birnin Beirut da su ka kasace a karkashin ikon dakarun kai daukin gaggawa.
Ana zargin rundunar kai daukin gaggawa da tafka laifukan yaki a cikin yankunan da a baya su ka shimfida ikonsu a ciki, har da babban birnin kasar Khartum.