HausaTv:
2025-04-14@17:56:15 GMT

Iran Za Ta Aike Da Tawaga A Matakin Koli Don Halartar Jana’izar Nasrallah

Published: 17th, February 2025 GMT

Iran ta bayyana cewa za ta aike da tawaga a matakin koli zuwa jana’izar mirigayi babban sakataren kungiyar Hizbollah ta kasar Lebanon Hassan Nasrallah.

Da yake sanar da hakan kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei ya ce kasar za ta halarci gagarumin bikin mai matukar muhimmanci,

Tunda farko dai kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da cewa tawagogin kasashe 79 za su halarci bikin tunawa da marigayi babban sakataren kungiyar Sayyid Hassan Nasrallah da kuma shugaban majalisar zartarwarta Sayyid Hashem Safieddine.

Sheikh Ali Daher, kodinetan babban komitin jana’izar Nasrallah da Safieddine, ya bayyana cewa bikin da aka shirya yi a ranar 23 ga watan Fabrairu, zai kasance “ranar tunawa da shugaban wanda aka zalunta a kan ma’abuta girman kai, da kuma shahidan bil’adama a kan mulkin mallaka”.

Ya kara da cewa jana’izar za ta ci gaba da zaburar da mutane masu ‘yanci a duniya shekaru da dama masu zuwa.”

Daher ya yi nuni da cewa bikin zai dauki kimanin sa’a daya kuma zai hada da jawabin babban sakataren kungiyar Sheikh Naim Qassem.

Sayyid Nasrallah ya yi shahada ne a yayin harin bam da Isra’ila ta kai a kudancin birnin Beirut a ranar 27 ga Satumba, 2024, Shi kuwa Safieddine ya yi shahada a lokacin harin da Isra’ila ta kai a watan Oktoban 2024.

Kungiyar Hizbullah ta dage bikin jana’izar shugabannin biyu saboda fargabar hare-haren Isra’ila a yayin bikin.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Dagewa Iran Takunkuman Zalunci Na Daga Cikin Manufofin Tattaunawa Da Amurka: Aref

Matainakin shugaban kasar kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya bayyana cewa, daukewa Iran takunkuman zalunci wadanda kasashen yamma suka dora mata na daga cikin asalin hakkin kasar da aka tauye.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aref yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma kara da cewa, kasar Iran ba zata manta da hakkin kasar wanda Amurka ta take tun farkon nasarar juyin juya halin kasar shekaru 46 zuwa yanzu ba, amma duk da haka sun bata damar tattaunawa.  Yace: Muna son mu nunawa duniya kan cewa har yanzun muna hakuri, amma ba zamu taba manta da zaluncin da aka yi mana ba.   Mataimakin shugaban yana maganar ficewar kasar Amurka daga yarjeniyar JCPOA da kuma dorawa kasar takunkuman tattalin arziki mafi muni da nufin kifar da gwamnatin kasar. Yace dukkan takunkuman tattalin arzikin da gwamnatocin kasar Amurka ta dorawa kasar tun bayan nasarar juyin juya halin kasar shekaru 46 da suka gabata basa bisa ka’ida.  Mataimakin shugaban kasar yana fadar haka ne bayan da ministan harkokin wajen kasar Abbas Aragchi ya kammala zagaye na farko na tattaunawa ba kai tsaye ba kan shirin makamacin Nukliya na kasar da tokwaransa na kasar Amurka Steve Witkoff a kasar Omman tare da ministan harkokin wajen kasar Omman Badr Hamad Al-Busaidi a matsayin mai shiga tsakani.

Iran Ta Godewa Omman Da Shiryawa Da Kuma Gudanar Da Tattaunawa  Tsakanin Amurka Da Iran

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Babban Daraktan Hukumar IAEA, Zai Ziyarci Iran ranar Laraba
  • Shugaban Kasar Iran Ya Mika Ta’aziyyar Ta Rasuwar Wanda Ya Assasa Hukumar  Makamashin Nukiliya Ta Iran
  • Iran Ta Ce Za’a Gudanar Da Zagaye Na Gaba Tsakaninta Da Amurka Ne A Birnin Roma Na Kasar Italiya
  • Kasashen Larabawa Na Yankin Tekun Farisa Sun Yi Fatan Al-Khairi Ga Iran Da Amurka A Tattaunawar Shirin Nukliyar Kasar
  • Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Dakatar Da Matakin Kare-Karen Harajin Fito Kan Hajojin Da Ake Shigarwa Kasar
  • Gwamnatin Amurka Ta Yi Da’war Cewa; Ba Ta Neman Tashin Hankali Tsakaninta Da Iran
  • Dagewa Iran Takunkuman Zalunci Na Daga Cikin Manufofin Tattaunawa Da Amurka: Aref
  • Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya godewa ministan harkokin wajen kasar Omman
  • Sharhi: Tattaunawa Zagaye Na Farko Tsakanin Iran Da Amurka A Oman
  • MDD: Mafi Yawancin Wadanda Yaki Ya Ci A Gaza Mata Ne Da Kananan Yara