Gwamnati Ta Buƙaci Sauƙaƙa Tsarin Samar Da Biza Don ƙarfafa Kasuwancin ‘Yan Nijeriya A Duniya
Published: 17th, February 2025 GMT
Ya ce: “A bara, na wakilci Nijeriya a Indonesiya, kuma na gano cewa akwai manyan kamfanoni hamsin daga Indonesiya da ke aiki a Nijeriya, amma ba mu da ko kamfanoni biyar daga Nijeriya da ke aiki a Indonesiya.
“Idan suna son zuwa ƙasar mu su yi kasuwanci saboda yawan mutanen mu da kuma damar da muke da ita na sayen kayayyakin su da ayyukan su, to ya kamata a samar da tsarin da zai ba da dama ga kamfanonin Nijeriya su ma.
Dangane da matsalar da ‘yan Nijeriya ke fuskanta bayan da gwamnatin Habasha ta soke tsarin nan na ‘e-visa’ da ‘Visa-on-Arrival’ ga matafiya daga Nijeriya, Idris ya tabbatar da cewa za a ɗauki matakin diflomasiyya ta hannun Ministan Harkokin Waje don magance matsalar.
Ministan ya bayyana cewa manufofin ba da biza a tsakanin ƙasashe na tafiya ne bisa tsarin da ke bai wa kowanne ɓangare dama daidai.
Ya ce ya zama dole ƙasashe su kasance masu adalci wajen aiwatar da manufofin da za su amfanar da ‘yan ƙasar su da na ƙasashen da suke hulɗa da su.
Ya ce: “Duk wata dangantaka da ƙasashen waje tana tafiya ne bisa tsarin amfanin juna. Idan muna ba su ‘Visa-on-Arrival’, babu dalilin da zai sa su hana mu ‘Visa-on-Arrival’.”
Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da ke zaune a ƙasashen waje da su kasance jakadu nagari, su nuna halaye nagari domin inganta sunan ƙasar.
“Ba ma yarda da mutanen da za su ɓata mana suna. Kuna da rawar da za ku taka, saboda ku ne ke zaune a nan. Idan ba ku wakilce mu da kyau ba, ba za a girmama mu ba. Ba wai ziyarar Shugaba Tinubu ko wani minista ce za ta gyara abin ba, amma ‘yan Nijeriya da ke zaune a nan ne za su iya gyara yadda duniya ke kallon ƙasar mu,” inji shi.
Idris ya kuma yi bayani kan sababbin manufofin da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa, inda ya ce an samu cigaba mai kyau a fannin farfaɗo da tattalin arziki, inganta ababen more rayuwa, yaƙi da rashin tsaro, da kuma dawo da ƙwarin gwiwar masu zuba jari a Nijeriya.
Ya ce Nijeriya ta samu jarin ƙetare na kusan dala biliyan 1.07 don kafa masana’antu da za su ƙera magunguna, matakin da zai taimaka wajen bunƙasa masana’antar magunguna a ƙasar, samar da ayyukan yi, da kuma ƙarfafa ɓangaren kiwon lafiya.
Haka nan, Ministan ya bayyana cewa a cikin kwanaki ƙasa da 250, an raba sama da naira biliyan 32 ga ɗalibai ƙarƙashin Shirin Lamunin Ɗalibai, domin tabbatar da cewa kowa na samun damar karatun boko ba tare da matsalar rashin kuɗi ba.
Dangane da ƙoƙarin yaƙi da rashin tsaro, Idris ya ce a shekarar 2024 kaɗai, jami’an tsaro sun kashe ‘yan ta’adda da ‘yan fashi 8,000, sun ceto mutane 8,000 da aka yi garkuwa da su, tare da cafke mutane 11,600 da ake zargi da aikata laifuka.
Har ila yau, ya tabbatar da cewa an kawar da ‘yan ta’adda daga hanyar Kaduna zuwa Abuja, wadda a da wurin aikata miyagun laifuka ce, lamarin da ya kawo sauƙi ga matafiya.
Da yake jawabi, Shugaban Al’ummar Nijeriya da ke Habasha, Muideen Alimi, ya ce suna shirin yin haɗin gwiwa da Hukumar Kula da ‘Yan Nijeriya Mazauna Ƙetare (NIDCOM) don shirya taron tattaunawa kan bunƙasa tattalin arziki ta hanyar kasuwanci tsakanin ƙasashen Afirka.
Ya buƙaci Nijeriya da ta goyi bayan shirin samar da Babban Bankin Afirka, tare da tabbatar da cewa Nijeriya ta taka muhimmiyar rawa a Hukumar Harhaɗa Kuɗaɗen Afirka (African Remittance Agency).
Taron ya samu halartar Darakta Janar ta Hukumar NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa, da wasu manyan jami’an gwamnati.
কীওয়ার্ড: tabbatar da cewa Nijeriya da ke a Indonesiya yan Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya godewa ministan harkokin wajen kasar Omman
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ila Bagaei ya godeawa ministan harkokin wajen kasar Omman kan yadda ya shirya ya kuma gabatar da tattaunawa tsakanin JMI da Amurka a birnin Mascat da kuma kai kawon da yayi a tsakanin bangarorin biyu.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Bagaei yana bayyana haka a wani sakon da ya aika a cikin shafinsa na X a jiya Asabar, ya kuma aika da sakon ne a dai dai lokacinda ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana kan hanyarsa ta dawowa Tehran, bayan tattaunawar. Ya kuma kara da cewa yana fatan Badr bin Hamad Al Busaidi zai ci gaba da wannan kokarin a ranar Asabar mai zuwa inda bangarorin biyu zasu sake haduwa, sannan har zuwa karshen tattaunawar. Bayan kammala tattaunawar dai, shugaban tawagar JKI a tattaunawar kuma ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana a shafinsa na X kan cewa, tattaunawar ta yi armashi.