Kasar Sin: Yankin Asiya Da Tekun Pasifik Ba Wajen Kartar Kasashe Masu Karfin Iko Ba Ne
Published: 18th, February 2025 GMT
A ranar 15 ga watan Fabrairu, ministocin harkokin waje na kasashen Amurka, Japan, da Koriya ta Kudu sun yi shawarwari a Munich na kasar Jamus. A cikin sanarwar hadin gwiwar da suka fitar, a karon farko, sun bayyana goyon bayansu ga yadda Taiwan za ta shiga cikin kungiyoyin kasa da kasa da suka dace, tare da jaddada muhimmancin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan.
Bugu da kari, a matsayin martani ga kwaskwarimar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi kan takardar sahihancin bayanai kan dangantakar Amurka da Taiwan, Guo Jia Kun ya bukaci bangaren Amurka da ya gaggauta gyara kuskuren, da kuma mutunta ka’idar Sin daya tak da sanarwoyi guda uku na Sin da Amurka, kuma ta bi a hankali wajen tinkarar batun Taiwan. (Mohammed Yahaya)
এছাড়াও পড়ুন:
Kwana Daya Bayan Kwace Fadar Shugaban Kasa, Sojojin Sudan Sun Kwace Babban Bankin Kasar
A ci gaba da shimfida ikonsu da suke yi a cikin birnin Khartum, sojojin Sudan sun kwace iko da babban bankin kasar, kwana daya bayan da su ka kori dakarun kai daukin gaggawa daga fadar shugaban kasa.
Kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya nakalto majiyar sojojin Sudan tana cewa; A yau Asabar sun yi nasarar kwace iko da babban bankin kasar, tare kuma da shimfida ikonsu a cikin wasu yankunan na birnin Khartum.
Kakakin sojan kasar Sudan Nabil Abdullah, ya bayyana cewa; Mun rusa sojoji da kayan aikin abokan gaba. Haka nan kuma Abdullah ya sanar da kwace wasu ma’aikatu da suke a tsakiyar birnin Beirut da su ka kasace a karkashin ikon dakarun kai daukin gaggawa.
Ana zargin rundunar kai daukin gaggawa da tafka laifukan yaki a cikin yankunan da a baya su ka shimfida ikonsu a ciki, har da babban birnin kasar Khartum.