IRGC: Za Mu Kai Farmakin “ Wa’adus-Sadik” Na 3 Akan ‘Yan Mamaya
Published: 18th, February 2025 GMT
Mataimakin kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran “IRGC” ya sanar da cewa; Iran za ta kai farmakin “Wa’adus-Sadik 3” a lokacin da ya dace.
Laftanar janar Ali Fadwi ya kuma yi ishara da yakin Gaza, yana bayyana cewa, su kansu ‘yan sahayoniya sun bayyana cewa Hamas ta yi nasara, su kuma ba su cimma manufarsu ba.
Iran dai ta kai wa HKI hare-hare guda biyu a aka bai wa Sunan “ Wa’adussadik” na daya da na biyu. Hare-haren na Iran dai sun kasance mayar da martani ne akan harin da HKI ta kai wa karamin ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Syria da kuma kashe mata jami’an soja masu bayar da shawara ga gwamnatin Damascuss. Na biyun kuwa ya kasance mayar da martani akan kisan gillar da ‘yan sahayoniyar su ka kawo a Tehran wanda ya yi sanadiyyar shahadar shugaban kungiyar Hamas Shahid Isma’ila Haniyyah.
A wani gefen, shugaban kungiyar Hamas a yankin Gaza, Khalil Hayyah ya fada a makon da ya shude cewa; Iran ta kasance a sahun gaba wajen taimakawa gwgawarmayar Falasdinu, kuma muna da tabbacin cewa za ta cigaba da yin hakan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Amurka Ta Yi Da’war Cewa; Ba Ta Neman Tashin Hankali Tsakaninta Da Iran
Gwamnatin Amurka ta sanar da cewa: Ba ta neman tada tashin hankali tsakaninta da Iran
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Samuel Werberg ya bayyana cewa: Kasarsa ba ta neman kara ruruta wutar rikici da Iran, yana mai jaddada cewa har yanzu kofar diflomasiyya a bude take, duk kuwa da kakkausar murya da Amurka ta yi na kin amincewa Iran ta mallaki makamin nukiliya.
Werberg ya kara da cewa; Za su ci gaba da riko da siyasar matsin lamba da nufin dakatar da ci gaba a shirin nukiliyar Iran.
Kakakin na Amurka ya bayyana cewa, “Dole ne Iran ta nuna kyakkyawar niyyarta kafin ta yi magana kan duk wata nasara da za a samu.