HausaTv:
2025-04-15@23:17:36 GMT

Sojojin HKI Sun Ce Ba Zasu Fita Daga Wurare 5 A Kudancin Kasar Lebanon Ba

Published: 18th, February 2025 GMT

Sojojin HKI Sun Bada sanarwan cewa ba zasu bar wasu tuddai guda 5 a kudancin kasar Lebanon ba, har zuwa wani lokacin da basu sani ba, saboda tsaron haramtacciyar kasar.

Tashar talabijin ta Almayadin ta  kasar Lebanon, ta nakalto cewa tankunan yakin HKI sun kutsa cikin garin kafarshuba na kudancin kasar Lebanon kuma sun kafa sansanin sojojin a garin.

A jiya litinin ce yakamata sojojin HKI su fice daga kudancin kasar Lebanon da suka mamaye, amma a jiyan din ne suka bada sanarwan cewa ba zasu fita daga wurare 5 daga kudancin kasar ta Lebanon ba.   

Kafin haka bayan kwanaki 60 da tsagaita budewa juna wuta ne, yakamata sojojin HKI su fice daga kudancin kasar ta Lebanon, amma tare da shiga tsakani na gwamnatin kasar Amurka, gwamnatin kasar Lebanon ta tsawaita wanzuwar sojojin yahudawan har zuwa yau Talata 18 ga watan Fabrayrun shekara ta 2025. A yau ne yakamata sojojin kasar Lebanon su karbi dukkan wuraren da sojojin yahudawan suke mamaye da su a kudancin kasar.

Har yanzun dai ba’a ji ta bakin gwamnatin kasar Lebanon dangane da wannan al-amarin.

Mai magana da yawan sojojin HKI sojojinsa ba zasu fita daga wadannan wurare 5 ba sabaoda tsaron HKI kuma a duk lokacinda suka ga mutanensu a yankin arewacin HKI zasu sami amince da zaman lafiya suna iya ficewa daga wadannan wurare.

Kafin haka dai babban sakatarin kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Qasim ya bayyana cewa sojojin HKI basu da wani uzuri na ci gaba da kasancewa a kudancin kasar Lebanon daga yau Talata 18 ga watan Fabrayrun shekara ta 2025

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: a kudancin kasar Lebanon

এছাড়াও পড়ুন:

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 109

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani  mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin Rumi, ko kuma cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

///.. Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan Almujtabah (a), lamami na biyu daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s) kuma da na farko ga Fatimah (s) diyar manzon All..(s).

A cikin shirimmu da ya gabata, mun   kawo maku kari daga dangin Khalifa Uthman wadanda ya dorasu kan musulni a kufa da Basra, da sham. Kuma sune Walidu dan Ukba da sa’id dan Ass da Abdullahi dan Amir da kuma Mu’awiya dan Abisufyan.

Munji yadda ko wanne daga cikinsu ya azabtar da mutanen da Khalifa ya dorasu a kansu, da kuma yadda Khalifa yake karesu. Sannan mun ji yadda Khalif Uthman ya karfafa Mu’awiya dan Abusufyan ya bashi karin larduna a sham, kuma ya bar masa dunkiyar sham gaba daya yana yin abinda ya ga dama. Sannan munga yadda ya shimfida masa hanya na zama khalifan musulmi da kuma yadda zai maida Khalifancin manzon All..(s) gado a cikin dangin banu umayya.

A yau ma bari mu dora daga kasar Masar, inda kafin haka, mun bayyana cewa Khalifa ya bawa Abdullahi ibn Abi-sharkh kudaden khumusin ganimar Afrika. Sannan daga baya ya sanya shi gwamnan kasar ya na yin abinda yaga dama, yana azabtar da musulmin kasar ya raya wanda ya ga dama ya kuma kashe wanda ya ga dama.

Sai dai kafin haka yakamata mu san ko waye Abdullahi ibn Abisarkh. Da farko ya musulunta tun kafin fatahin makka, yayi hijira zuwa Madina, sannan manzon All..(s) ya sanya shi daga cikin wadanda suke rubuta masa ayoyin al-qur’ani idan suka sauko.

Daga nan sai wata rana All..T ya sauko masa da ayoyi a cikin Suratul  Muminun inda yake cewa:

{Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halicci mutum daga wani tsantsa daga lãka. Sa’an nan kuma Muka sanya shi, ɗigon maniyyi a cikin matabbata natsattsiya.

Sa’an nan kuma Muka halicce shi gudan jini, sa’an nan Muka halicci gudan jinin tsõka, sa’an nan Muka halicci tsõkar ta zama ƙasũsuwa, sa’an nan Muka tufãtar da ƙasũsuwan da wani nãma sa’an nan kuma Muka ƙãga shi wata halitta dabam. … a lokacin da ya kai wannan gabatar, sai Abdullahi dan abi Sharkh ya yi mamakin yadda All..T ya halicci mutum.. sai ya rika manazon All..fadar  “Sabõda haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne Mafi kyaun mãsu halittawa… sai manzon All..(s) ya ce masa, (ka rubuta, kamar yadda ka fada, don haka ta sauka}.

Daga nan sai Abdullahi dan Abi Sarkh ya fara shakkar manzon All..(s) ya na cewa: Idan Muhammadu (s) mai gaskiya ne, to ni ma an yi mani wahyi kamar yadda aka yi masa, idan kuma ba mai gaskiya ne ba,  shi ba annabi ba ne, to na fadi abinda ya fada ni ma an yi mani wahyi. Daga nan sai Abdullahi ya yi ridda ya koma Makka yana’ isgili da manzon.

Bayan haka sai wanan aya 93 ta suratul An’am ta sauka tana kafirta shi , wato insa All.. yake cewa:

{Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ce: “An yi wahayi zuwa gare ni,” alhãli kuwa ba a yi wahayin kõme ba zuwa gare shi ba, da wanda ya ce: “zan saukar da misãlin abin da Allah Ya saukar?” Kuma dã kã gani, a lõkacin da azzãlumai suke cikin mãyen mutuwa, kuma malã’iku sunã mã su shimfiɗa hannayensu, (sunã ce musu) “Ku fitar da kanku; a yau anã sãka muku da azãbar wulãƙanci, sabõda abin da kuka kasance kunã faɗa, sabanin gaskiya, ga Allah kuma kun kasance daga ãyõyinSa ku nã yin girman kai.”}

Malaman tafsiri sun gamu kan cewa wannan ayar ta sauka ne, kan Abdullahi dan Abi sarkh bayan yayi rikka ya koma makka yana isgili da manzon All…(s).

Kuma wannan ya faru ne kafin fatahin Makka, don haka a lokacinda manzon All..(s) ya kwace Makka, sai ya bada umurnin a kashe wasu mutane ko an samesu suna rike da Kellen dakin Ka’ab, Abdullahi ibn Abi sarkh yana daga cikinsu saboda riddan da yayi da kuma isgilin da yakewa manzon All..(s) bayan ya sake komawa cikin mushrikai.

Bayan wannan umurnin da manzon All..(s) ya bayar a ranar Fatahin Makka, sain Uthman dan Affan ya yi sauri ya nemo shi, ko kuma Abdullahi ya nemi shi Uthman, ya je ya moye shi a wani wuri, sai da abubuwa suka lafa a Makka, sai ya fito da shi ya zo da shi gaban manzon All..(s) ya na neman masa gafara, kuma ya sake dawowa cikin addinin musulunci.

Don haka a lokacinda Uthman ya gabatar da shi gaban manzon All..(s), ya ne neman masa Afwa, sai manzon All…(s) ya dade bai yi magana ba, sai daga karshe ya ce ya amince ya gafarta masa.

A lokacin da  Uthman ya tashi ya tafi tare da shi, sai manzon All..(s) ya cewa wadanda suke tare da shi : Me yasa wani daga cikinku bai tashi ya sare wuyarsa ba?, Sai wani sahabi mutumin ansar ya ce masa, Ya Manzon All..(s) da ka yi mana ishara! da mun sare wuyarsa, sai yace, ai mu annabawa basa ‘kha’ince da idanunsu.

To wannan mutum ne fa, Khalifa Uthman, wanda manzon All..(s) ya halatta jininsa ko da yake rike da rigar dakin Kaaba, kuma yana fatan da wani ya buge wuyarsa a lokacin da Uthaman ya kawo shi, bayan kimanin shekaru 13 da wafatin manzon All..(s) Khalifa Uthman ya bashi gwamnan kasar Masar.

Kafin haka ya bashi dukiya mai yawa don shi dan’uwansa na shayarwa ne, yana azabtar da su yana kashe su. Da abun yayi yawa, sai da farko tada mutum guda daga cikinsu ya je madina ya fadawa manya manyan sahabban manzon All..(s) wadanda suka hada da Talha da Zubair da Imam Ali (a) da kuma A’isha matar manzon All.. (s), suka je suka yiwa Khalifa magana, wasu kuma sun ce Imam Ali kawai ya fadawa irin halin da suke ciki, da  yadda dan uwan Khalifa Abdullahi dan abi sarkh yake wahalar da su.

A lokacinda suka yi masa magana, sai Khalifa ya rubuta masa wasika inda a cikinta ya yabukace shi ya sauya halinsa ko kuma ya tube shi. Amma ya karbi wasikar ya karantata, bai tuba ba, bai kuma sauya halayensa. Banda haka, a lokacinda ya gano wanda ya kai kararsa wajen Khalifa  sai ya sa aka kashe shi.

A nan ne sai mutanen Masar suka tura mutane 700 zuwa madina, su je, suka ga na da manya manyan sahabban manzon All..(s) suka kara bayyana masu halin da suke ciki.

A wannan karon Aliyu dan Abitalib (a) ya shiga wajensa ya yi masa, wato Khalifa magana, kan ya sauya masu wannan mutum da wani.

A nan sai Khalifa Uthman ya amince, ya ce masu su zabi duk wanda suke so, ya sauya masu da shi. Sai suka zabi Muhammad dan Abubakar wani matashi dan shekara kimani 26 a duniya amma, ya girma ya kuma tashi a gidan Imam Ali(a) ya sami tarbiyya mai kyua da kuma Ilmi mai yawa, saboda mahaifiyarsa Asma’u diyar Umais ta auri Imam Ali(a) bayan wafatin Khalifa na farko, a lokacin da mahammadu dan Abubakar ya na tsakanin shekara 3 zuwa 4 a duniya.

Daga nan sai Khalifa ya rubuta masu wasika,  kan cewa, ya tube Abdullahi ibn Abi sarkh, sannan ya nada Muhammad dan Abubakar a matsayin gwamna ko walin kasar Masar.

Daga nan sai suka kama hanya dauke da wadannan wasiku tare da kuma sabon gwamnan kasar ta Masar.

Mutanen 700 sun yi tafiya har sai da suka isa wani gari da ake kira ‘Al-hums’, kan hanyar masar, sai suka fahinci cewa akwai wani mutum wanda ya isa garin daga Madina, a lokacinda ya karasa cikin garin, sai suka gano shi bawan khalifa Uthman ne,  mai suna ‘Warsh’, yana kuma hanye da dokin fadar Khalifa, Sai suka yi shakkarsa.

Wasu sun ce, sun tambayeshi ina za shi ? Sai ya ce kasar Masar, sai suka ce me zaka yi, sai ya ce, zai kaiwa gwamna sako daga Khalifa, sai suka ce ma sa ai ga sabon gwamnan masar nan yana tare da mu, sai yace ba wannan ba. Kaga Kenan yana nufin Abdullahi dan Abi Sarkh.

A nan sai suka binciki kayansa, har sai da suka fito da wata wasika, da sunan Khalifa Uthman da Khatiminsa zuwa dan uwansa Abdullahi dan Abisarkh, kan cewa idan wadannan mutane 7000 su zo ya kashesu gaba daya.

Sannan suka gano cewa, rubutun hannun Marwan dan Hakam ne, sakataren gwamnatin Khalifa Uthman. Daga karshe dai suka kama wannan bawan Khalifa mai suna Warsh, suka koma da shi madina, da nufin, tilasta masa sauka daga kujerar Khalifanci, idan kuma yaki su kashe shi.

Don haka Khalifa ya bawa Abdullahi dan Abusarkh dama wacce ta wuce gona da Iri, har sai da ta kai ga ya rasa ransa saboda hakan.

Mutum wanda ayoyin al-kur’ani mai girma suka sauka suna tabbatar da kafircinsa, amma duk tare da cewa ya sake dawowa musulnci, wa ya san ko All..ya karbi tubansa ko bai karbaba?.

Banda haka kissan sa ya haddasawa al-ummar Musulmi fitina a bayansa, wanda ya raba kan musulmi, ya kuma bawa shaidanu daga cikin danginsa, wadanda daga baya suka, sallada kansu, kan musulmi, kuma suka sami damar kwace iko daga hannun bayin All..daga kuma iyalan gidan manzon All..(s). wato Imam Hassan Almujtaba dan Ali (a). Kuma sun yi kokarin sauya fahinta da Akidar addinin musulunci kamar yadda aka sauko da shi.

Kamar yadda zamu gani nan gaba, mutuwa ko kissan Khalifa Uthman ya yi sanadiyyar rabuwar kan musulmi zuwa Sunna da Shia, kungiyoyi biyu wadanda basa ga maciji tun lokacin har zuwa yanzu shekaru fiye da 1,400, kuma da alamun wannan halin zai ci gaba har sai allama sha’allahu.

Khalifa Uthman yayi shekaru kimani 12 yana khalifanci kafin a kashe shi, kuma kamar yada zamu gani sahabban manzon All…(s) wadanda suka hada da Talha dan Ubaidullahi, da Zubair dan Awwam da kuma ummul muminina Aisha, suna daga cikin wadanda suka bayyana rashin amincewarsu da yadda ya gudanar da khalifancinsa suka kuma ingiza mutane masu adawa da shi suka kashe shi.

Don haka da dama sun ji dadi da aka kashe shi. Sai dai, bayan kasheshi mutane sun zami Imam Ali (a) a matsayin khalifa a bayansa. Amma wadan nan sahabban suka juya suka ce ai, Imam Ali (a) ne ya kashe Uthman ko kuma yana tare da wadanda suka kashe Uthman.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barkatuhu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ana barazanar korar sojojin Isra’ila da ke neman a kawo ƙarshen yaƙin Gaza
  • Rasha Ta Sanar Da Kashe Manyan Kwamandojin Sojin Ukraine Fiye Da 60 A Birnin Sumy Na Kasar Ta Ukraine
  • An Kashe Sojojin Yahudawa A Gaza A Yayinda Wasu Da Dam Suka Ji Rauni
  • Sojoji sun ceto mafiya 16 da aka yi garkuwa da wasu a Filato
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 109
  • An yi garkuwa da masu ibada a Kogi
  • Sojojin Yemen Sun Kakkabo Jirgin Yakin Amurka Wanda Ake Sarrafa Shi Daga Nesa Na 19
  • Dagewa Iran Takunkuman Zalunci Na Daga Cikin Manufofin Tattaunawa Da Amurka: Aref
  • Ukraine na Fuskantar Wata Barazana, Dangane Da Bukatar Amurka Na Kwace Iko Da Cibiyar Gas Na Rasha  A cikin Kasar
  • Jiragen Yakin Kasar Amurka Suna Rusa Cibiyoyin Ilmi A Hare-Haren Da Suke Kaiwa Kasar Yemen