A ranar Asabar din da ta gabata ne shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Afirka AU, suka zabi shugaban kasar Angola Joao Lourenco, a matsayin sabon shugaban karba-karba na kungiyar da kuma ministan harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa na Djibouti, Mahamoud Ali Youssouf, a matsayin sabon shugaban hukumar gudanar da ayyukan kungiyar, wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a kasashe biyu masu matukar muhimmanci a nahiyar, wato Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo (DRC) da kasar Sudan.

Rikicin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo na kara kamari, bayan samun galaba a wasu yankunan kasar da ‘yan tawayen M23 suka yi, na baya-bayan nan shi ne kwace iko da muhimman wurare da dama a birnin Bukavu, hedkwatar lardin Kivu ta kudu, da safiyar ranar Asabar, ciki har da gidan gwamnan lardin, makonni biyu bayan kwace babban birnin Goma. DRC dai ta zargi kasar Rwanda da marawa ‘yan tawayen baya, amma Rwanda ta musanta wannan zargin. Tun daga wannan lokacin kawo yanzu, shugabannin nahiyar ba su daina yin kiraye-kiraye da a tsagaita wuta ba tare da wani sharadi ba, da dakatar da tashin hankali da kuma bude manyan hanyoyin samar da kayayyaki da filin jirgin Goma ba. Hakazalika, Sudan ita ma ta kasance wata babban jigon tashe-tashen hankula da shugabannin nahiyar ke tattaunawa. Tsananin wadannan rikice-rikice na iya haifar da yakin yanki, ganin cewa sojojin kasashe makwabta, kamar Afirka ta Kudu sun riga sun shiga kasar Congo Kinshasa. Idan ba mu manta ba, tun bayan manyan yake-yake guda biyu wadanda suka faru tsakanin 1996 zuwa 2003, wanda ya hada da kasashe kusan goma na Afirka, ake zaman dar-dar a gabashin Congo Kinshasa, wanda kuma ke barazanar sake haifar da rikicin kabilanci da na siyasa a yankin manyan tabkuna.

Kungiyoyin kasa da kasa da masu ruwa da tsaki sun yi gargadin cewa idan ba a yi taka tsantsan ba, wannan rikici na iya rikidewa zuwa yakin yanki, sun nakalto bakar azabar da aka fuskanta a tashe-tashen hankulan shekarun 1990. Hakazalika, al’ummar kasa da kasa na fatan sabon shugabancin AU zai dauki kwararan matakai da inganta hadin gwiwa, don kwantar da hankula, da samar da kyakkyawan martani ga duk wani rikicin da ke addabar nahiyar.

 

 

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

 Haaretz: Sojojin Isra’ila Suna Kan Shirya Kai Wa Gaza Hari Ta Kasa

Jaridar HKI ta “Haaretz” ta buga wani labara da yake cewa, sojojin HKI suna shirin kai wa Gaza gagarumin hari ta kasa bisa cikakken goyon bayan Donald Trump na Amurka.

Jaridar ta kuma ce; Harin na kasa da sojojin za su kai a cikin zirin Gaza,gagarumi ne a karkashin sabon babban hafsan hafsoshin soja Iyal Zamir.

 Har ila yau, marubucin rahoton Amos Har’el ya kuma kara da cewa; A wannan karon sun yi imani da cewa gagarumin harin da za su kai wa Gaza zai sa su cimma manufofin da su ka sanya a gaba da aka kasa a cikin tsawon shekara daya da rabi.

Daga cikin wadannan manufofin da ‘yan sahayoniyar suke son cimmawa da akwai rusa makamai da karfin kungiyar Hamas.

Jaridar ta kuma ce a daidai lokacin da ake maganar tattaunawa domin musayar fursunoni, HKI tana shirin sake amfani da karfin soja domin sake shimfida ikonta a cikin Gaza baki daya.

Danagne da rawar da Amurka take takawa a cikin abubuwan da suke faruwa, iyalan fursunoni wadanda suke da takardun zama, ‘yan Isra’ila a lokaci daya kuma Amurkawa, gwamnatin Amurka ba sanar da su cewa, Donald Trump yana cikin shirin bai wa Benjamine Netanyauhu cikakken goyon bayan idan ya zartar da fara kai hare-hare ta kasa akan Gaza. Haka nan kuma an sanar da cewa, ko kadan Trump ba zai yi wa Netanyahu matsin lamba akan dole sai ya koma kan batun musayar fursunoni ba ta ruwan sanyi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalilin da dimokuraɗiyya ta gaza kawo ci gaba a Afirka — Obasanjo
  • Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Lebanon Ya Ce Basa Da Wani Shiri Na Samar Da Haldar Jakadanci Da HKI
  • Wajibcin Gina Al’ummar Duniya Mai Kyakkyawar Makomar Bai Daya
  • Ana ci gaba da gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falastinu a kasashen duniya
  • An Bude Taron Shekara-Shekara Na Dandalin Tattauna Raya Kasa Na Sin Na 2025
  • Iran Tace Zata Kaddamar Da Sabbin Magunguna Da Ta Samar Tare Da Amfani Da Makamashin Nukliya
  • Za’a Gudanar Taron Tattaunawa Tsakanin Rasha Ta Amurka A Karo Na Biyu 2 A Birnin Rayad na Kasar Saudiya
  • Wakilin Sin Ya Yi Bayani Game Da Tunanin Sin Kan Kare Hakkin Dan Adam Da Kin Amincewa Da Siyasantar Da Hakkin Dan Adam
  •  Haaretz: Sojojin Isra’ila Suna Kan Shirya Kai Wa Gaza Hari Ta Kasa
  • Kwana Daya Bayan Kwace Fadar Shugaban Kasa, Sojojin Sudan Sun Kwace Babban Bankin Kasar