Kasar Iran Zata Aika Da Tawaga Mai Karfi Zuwa Jana’izar Sayyid Nasarallah
Published: 18th, February 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’el Baghae ya ce gwamnatin kasar Iran zata aika tawaga mai karfi zuwa kasar Lebanon don halattar Jana’izar Sayyid Hassan Nasarallah wanda za’a gudanar a cikin yan kwanaki masu zuwa.
Bakha’I ya kara da cewa, zamu halarci Jana’izar a kasar Lebanon, kuma zamu aika da tawaka wacce zata kunshi manya-manyan jami’an gwamnati da kuma malaman addini.
A ranar Talatan da ta gabata ce wani jami’an kungiyar ta Hizbullah, ya bada sanarwan cewa baki daga kasashe 79 ne zasu halarci jana’izar.
Sheikh Ali Daher shugaba kwamitin gudnar da jana’izar ya kara da cewa, ranar zata kasashen ranar sabonta bai’a da marigayin da kuma wanda ya gaje shi.
A ranar 27 ga watan Satumba shekara ta 2024 ne jiragen yakin HKI suka sauke ton 85 da boma-bomai a kan shugaban kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah wanda ya kai ga rasa ransa..
annan bayan yan kwanaki suka kashe magajinsa, Sayyis Safiyuddeen.
A cikin watan Octoba ne sojojin yahudawan suka kashe Shahid Sayyid Safiyyud, amma za’a hada Jana’izar shuwagabannin biyu a rana guda, amma za’a rufe su a a wurare daban-daban.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ba Ta Da Niyyar Tattaunawa Da Amurka A Fili Bainar Jama’a Kan Shirinta Na Makamashin Nukiliya
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ba su da niyyar gudanar da tattaunawa da Amurka a fili
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana ta shafinsa na Twitter a takaitaccen jawabin da aka shirya yi a taron manufofin nukiliya na kasa da kasa na Carnegie, yana mai jaddada cewa, “Iran sam ba ta da niyyar yin shawarwari da Amurka a fili a bainar jama’a.”
Araghchi ya rubuta a shafinsa na Twitter da safiyar yau Talata cewa, “Lokacin da ya amince da gabatar da muhimmin jawabi a taron manufofin nukiliya na kasa da kasa na Carnegie, har yanzu Iran da Amurka ba su sanya ranar da za a yi shawarwarin zagaye na gaba ba, wanda za a fara a matakin kwararru a ranar Laraba da kuma babban mataki a ranar Asabar.
Ya kara da cewa, “Kamar yadda ya jaddada a cikin jawabinsa da ya shirya, ko kadan Iran ba ta da niyyar yin shawarwari a fili a bainar jama’a.” Araghchi ya ci gaba da cewa, “A cikin jawabinsa, ya kuma bayyana karara cewa wasu ‘kungiyoyin masu sha’awa na musamman’ na kokarin yin magudi tare da bata tsarin diflomasiyya ta hanyar bata sunan masu tattaunawan tare da yin kira ga gwamnatin Amurka da ta gabatar da bukatu mafi tsanani da girma.”