Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza

Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan Zirin Gaza, wanda ya shafe tsawon watanni 15 kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni a watan Janairun da ya gabata.

A cewar jaridar, sojoji 15,000 da ke cikin sojojin mamayar Isra’ila suka jikkata tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, yayin da wasu 846 suka sheka lahira.

Daga cikin wadanda suka samu raunuka, sojoji 8,600 ne suka sami raunuka daban-daban na jiki, yayin da wasu 7,500 suka samu matsalolin tabin kwakwalluwa ciki har da firgita, damuwa, tashin hankali, rikirkicewar tunani, kamar yadda jaridar ta nakalto daga sashin  kula da dabi’ar ma’aikata da ke karkashin Ma’aikatar yakin haramtacciyar kasar Isra’ila.

Kanun labarai

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Isra ila ta

এছাড়াও পড়ুন:

Sama da mutane 1,560 ne sukayi shahada tun bayan da Isra’ila ta koma kai farmaki Gaza

Jami’an lafiya a Gaza, sun ce akalla mutane 1,563 ne aka kashe tun bayan da Isra’ila ta koma kai farmaki a Zirin tun daga ranar 18 ga watan Maris, yayin da al’amuran jin kai ke kara ta’azzara a Gaza.

Adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza tun bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas ta Falasdinu a watan jiya ya zarce 1,560 a cewar jami’an kiwon lafiya.

A cikin wata sabuwar sanarwa da ta fitar yau Asabar, ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce hare-haren Isra’ila sun kashe akalla mutane 21 a cikin sa’o’i 24 na baya-bayan nan.

An kashe mutane 50,933 tare da raunata 116,045 tun farkon yakin a watan Oktoban 2023, in ji ma’aikatar a alkalumman data sabunta.

A cewar hukumar ‘yan gudun hijira ta Falasdinawa UNRWA, kimanin Falasdinawa 400,000 ne aka tilastawa barin muhallansu a fadin Gaza tun bayan da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta fara aiki a watan Janairu ta ruguje kusan wata guda da ya gabata.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jiragen Yakin Kasar Amurka Suna Rusa Cibiyoyin Ilmi A Hare-Haren Da Suke Kaiwa Kasar Yemen
  • Sama da mutane 1,560 ne sukayi shahada tun bayan da Isra’ila ta koma kai farmaki Gaza
  • Isra’ila ta yi barazanar fadada hare-hare Gaza yayin da ta yanke Rafah daga birnin Khan Yunis
  • Me Ya Janyo Jifan Mawaka A Arewacin Nijeriya?
  • Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro
  • Hizbullah ta kirayi gwamnatin Lebanon da ta dauki mataki kan hare-haren Isra’ila
  •  Sojojin HKI Sun Yi Kisan Kiyashi A Yankin Shuja’iyya
  • Gwamnati ta gargaɗi jihohi 30 kan ambaliyar ruwa
  • Sin Ba Za Ta Razana Da Zuwan Yakin Cinikayya Ba
  • Sojojin Sama Na HKI Kimani 1000 Guda New Suka Bukaci A Kawo Karshen Yaki A Gaza