Shugaban Amurka Ya Ce: Sun Baiwa Fira Ministan Gwamnatin Isra’ila Damar Ya Aikata Abin Da Yake So
Published: 18th, February 2025 GMT
Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya aikata duk abin yake so
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi nuni da wa’adin da ya bayar dangane da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma sakin fursunonin, yana mai cewa ya shaidawa fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya aika duk abin da yake so.
Trump ya tabo batun mataki na gaba – ana sa ran za a fara tattaunawa nan ba da jimawa kan kashi na biyu na yarjejeniyar – ya ce: “Ya rage ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan mataki na gaba, tare da tuntubarsa.”
An kuma tambayi Trump ko jinkirin jigilar makamai zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila a karkashin Shugaba Biden zai “hana tsagaita bude wuta?,” inda ya amsa da cewa: “Wannan ana kiransa zaman lafiya ta hanyar karfi.
Kalaman na zuwa ne bayan da Netanyahu ya sanar da cewa zai kira taro domin tattaunawa kan mataki na biyu na yarjejeniyar da ya kamata a bude makonni biyu da suka gabata.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Haaretz: Sojojin Isra’ila Suna Kan Shirya Kai Wa Gaza Hari Ta Kasa
Jaridar HKI ta “Haaretz” ta buga wani labara da yake cewa, sojojin HKI suna shirin kai wa Gaza gagarumin hari ta kasa bisa cikakken goyon bayan Donald Trump na Amurka.
Jaridar ta kuma ce; Harin na kasa da sojojin za su kai a cikin zirin Gaza,gagarumi ne a karkashin sabon babban hafsan hafsoshin soja Iyal Zamir.
Har ila yau, marubucin rahoton Amos Har’el ya kuma kara da cewa; A wannan karon sun yi imani da cewa gagarumin harin da za su kai wa Gaza zai sa su cimma manufofin da su ka sanya a gaba da aka kasa a cikin tsawon shekara daya da rabi.
Daga cikin wadannan manufofin da ‘yan sahayoniyar suke son cimmawa da akwai rusa makamai da karfin kungiyar Hamas.
Jaridar ta kuma ce a daidai lokacin da ake maganar tattaunawa domin musayar fursunoni, HKI tana shirin sake amfani da karfin soja domin sake shimfida ikonta a cikin Gaza baki daya.
Danagne da rawar da Amurka take takawa a cikin abubuwan da suke faruwa, iyalan fursunoni wadanda suke da takardun zama, ‘yan Isra’ila a lokaci daya kuma Amurkawa, gwamnatin Amurka ba sanar da su cewa, Donald Trump yana cikin shirin bai wa Benjamine Netanyauhu cikakken goyon bayan idan ya zartar da fara kai hare-hare ta kasa akan Gaza. Haka nan kuma an sanar da cewa, ko kadan Trump ba zai yi wa Netanyahu matsin lamba akan dole sai ya koma kan batun musayar fursunoni ba ta ruwan sanyi.