Za a binciki INEC kan jinkirin gudanar da zaɓen cike giɓi
Published: 18th, February 2025 GMT
Majalisar Wakilai ta umarci kwamitinta kan harkokin zaɓe da ya binciki Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC dangane da jinkirin da take yi na gudanar da zaɓen cike giɓin wasu kujerun ’yan majalisar tarayya da na jihohi.
Majalisar a wannan Talatar ta kuma bayyana cewa jazaman ne kwamitin ya gayyaci Hukumar INEC domin ta bayar da dalilai kan tsaikon da aka samu da kuma yadda take ƙoƙarin yi wa tufkar hanci.
Aminiya ta ruwaito cewa Majalisar ta buƙaci kwamitin ya sauke wannan nauyi tare da miƙa mata rahoton bincikensa nan da makonni huɗu.
Wannan dai na zuwa ne bayan ƙorafin da wani ɗan majalisar, Jafaru Leko ya gabatar yana mai kafa hujja da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya wanda ya ɗora wa INEC alhakin gudanar da zaɓe a faɗin ƙasar.
Kazalika, ya naƙalto sassa na 47 da 90 da ke cikin Kundin Tsarin Mulkin wanda ya hukunta assasa majalisun tarayya da na jihohi a matsayin wani rukuni na ’yancin ’yan ƙasa su samu wakilci.
Ya yi ƙorafin cewa tun bayan Zaɓen 2023 da waɗanda suka biyo baya, an samu giɓi a majalisun tarayya da na jihohi saboda wasu dalilai kamar mutuwa, karɓar wasu muƙaman ko ajiye aiki.
Jafara Leko ya ci gaba da ƙorafin cewa Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya yi tanadin gudanar da zaɓen cike giɓi cikin tsawon lokacin da bai gaza wata guda ba da samun giɓin.
Ya ƙara da cewa, gudanar da zaɓen wanda alhakinsa ya rataya a wuyan Hukumar INEC shi ne zai tabbatar da wakilcin kowace mazaɓa a ƙasar.
A cewarsa, wannan jinkiri da INEC take ci gaba da yi rashin biyayya ne ga Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, lamarin da ke cutar da al’umma ko mazaɓar da ba su wakilci a hukumance.
Aminiya ta ruwaito cewa, a halin yanzu akwai kujerun ’yan Majalisar Tarayya bakwai masu giɓi da suka haɗa da na Majalisar Wakilai biyar da kuma biyu a Majalisar Dattawa.
Kujerun da ke da giɓi a Majalisar Wakilan sun haɗa da na jihohin Edo, Oyo, Kaduna, Ogun da Jigawa sai kuma na Majalisar Dattawa da suka ƙunshi Edo da Anambra.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Wakilai Zaɓe Kundin Tsarin Mulkin gudanar da zaɓen a Majalisar
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Xi Ya Yi Kira Ga Sin Da Vietnam Da Su Wanzar Da Daidaito A Tsarin Rarraba Hajoji
A nasa bangare kuwa, To Lam cewa ya yi Vietnam a shirye take ta yi aiki tukuru don kyautata tsare-tsare da hadin gwiwa da bangaren Sin ta yadda za a daga martabar cudanyar sassa daban daban, da nacewa ka’idoji 5 na zaman jituwa, da kare dokokin gudanar da cinikayya na kasa da kasa, da martaba yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin sassan biyu, da hada hannu wajen ba da gudummawa ga wanzuwar zaman lafiya da ci gaban daukacin bil’adama. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp