Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alhinin Rasuwar Edwin Clark
Published: 18th, February 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya tayi matukar alhinin rasuwar Dattijo kuma Tsohon Kwamishinan Yada Labarai na Tarayya, Cif Edwin Clark, wanda ya rasu yana da shekaru casa’in da bakwai.
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja.
Ya ce, Marigayi Cif Clark gwarzo ne mai kishin kasa, mai fafutukar tabbatar da adalci da gaskiya, kuma ginshiki ne a ci gaban dimokuradiyyar Najeriya.
Mohammed Idris, ya kara da cewa, Marigayi ya sadaukar da kansa wajen bautawa kasa a fannoni da dama, musamman a matsayin shi na ɗan siyasa da mai kishin kasa, wanda ya bar gagarumar alama a harkokin mulki, hadin kai, da ci gaban Najeriya.
“Fafutukarsa da hikimarsa da jajircewarsa wajen ci gaban kasa sun sa, ya zama murya mai matukar tasiri a siyasar Najeriya,” in ji Minista.
“Za a yi matukar rashin shawarwarinsa masu hikima da gudunmawarsa wajen gina kasa.”
“Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan Cif Clark, gwamnatin da al’ummar Jihar Delta, da dukkan ‘yan Najeriya da suka amfana da rayuwarsa mai albarka. Muna rokon Allah Ya jikansa, Ya kuma bai wa iyalansa da duk masu jimamin wannan rashi babban hakuri da karfin zuciya.”
Rel/Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Clark Gwamnatin Rasuwar Tarayya
এছাড়াও পড়ুন:
Iran da Amurka zasu ci gaba da tattaunawa a mako mai zuwa
An kammala zagayen farko na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a babban birnin Muscat a shiga tsakanin kasar Oman.
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da Steve Witkoff, manzon musamman na shugaban Amurka kan harkokin yankin gabas ta tsakiya ne suka jagoranci shawarwarin yau Asabar.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar ta ce bangarorin sun yi musayar ra’ayi game da shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya, da kuma dage takunkumi.
Ya kara da cewa an gudanar da shawarwarin ne cikin yanayi mai ma’ana kuma bisa mutunta juna.
A karshen sama da sa’o’i biyu da rabi na tattaunawar, shugabannin tawagogin Iran da na Amurka sun yi jawabi na ‘yan mintoci kadan a yayin da suke barin wurin taron a gaban ministan harkokin wajen Omani,” in ji ma’aikatar.
Bangarorin kuma zasu sake tattaunawa nan da mako mai zuwa, saidai ba’a bayyana takaimaimai wajen da tattauanwar za ta wakana ba.
A gefen tattaunawar, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmaeil Baghaei ya shaidawa kafar yada labarai ta IRIB a birnin Muscat cewa, Iran na da manufa guda daya tabbatar da muradun kasa.