Tara Daga N100,000 Kan Amfani Da Mitar Wutar Lantarki Ta Ɓarauniyar Hanya – NERC.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [13]

Ibnu Juzai al-Kalbi Allah Ya yi masa ranama yan nuna mana munin hassada ta fuska biyu:

1. A Ɗabi’a: Hassada tana haifar da cutar zuciya, wadda ke hana mutum farin ciki da jin daɗin rayuwa, kuma tana sa mai yin ta ya zama mai mugun hali, da ƙoƙarin ganin wani ya faɗi ko ya rasa abin da ya samu. A al’ada, mutane suna ƙin mai hassada saboda halayensa na rashin son alheri ga mutane da kuma fatan sharri a gare su.

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [12] Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [11]

2. A Shari’a: A cikin Alƙur’ani, Allah ya yi umurni da a nemi tsari a wurinsa daga hassadar mahassadi, inda Ya ce:” Ka ce:” Ina neman tsari da Ubangijin asuba. Daga sharrin abin da Ya halitta. Da kuma sharrin dare idan ya lulluɓe da duhu. Da kuma sharrin mata masu tofi a cikin ƙulle-ƙulle. Da kumma sharrin mahassadi yayin da ya yi hassada.” Suratul Falaƙ aya ta 1-5. Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Kada ku yi hassada da juna…” Muslim ne ya ruwaito [#2563].

Hassada tana iya kai mutum ga saɓawa Allah, kamar yadda Shaiɗan ya ƙi yin sujada ga Adam saboda kishi da hassada. Hassada tana haifar da cin amanar ‘yan’uwa, da munafunci, da karya. Hassada tana cutar da mai yin ta fiye da wanda ake yi wa. A ɗabi’a, tana hana kwanciyar hankali, a shari’a kuwa tana kai mutum ga zunubi. Maimakon yin hassada, Musulumi ya kamata ya roƙi Allah ya ba shi alheri kamar yadda Ya ba wa waninsa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Tace Zata Kaddamar Da Sabbin Magunguna Da Ta Samar Tare Da Amfani Da Makamashin Nukliya
  • Gombe Za Ta Kashe Naira Biliyan 1.1 Don Samar Da Fitilun Hanya Masu Aiki Da Hasken Rana
  • Matasa sun kashe yaron da suka yi garkuwa da shi a Bauchi
  • EFCC Ta Cafke Mutum 21 Bisa Zarginsu Da Zambar Intanet A Bauchi
  • Gwamnatin Jigawa ta ƙaddamar da shirin noman rani na Lallashi
  • Matasa 4 Sun Yi Garkuwa Da Yaro, Sun Kashe Shi A Bauchi
  • Za a hukunta ma’auratan da suka ci zarafin yarinya a kan mangwaro — Zulum
  • El-Rufa’i Ya Yi Kadan Ya Sa Mu Bar Jam’iyyar PDP – Sule Lamido
  • An Bukaci Gwamnati A Kowani Mataki Da Ta Taimakawa Yaki Da Shan Magani Ba Bisa Ka’ida Ba
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [13]