Majalisa ta tsayar da ranar sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin Dokar Haraji
Published: 19th, February 2025 GMT
Majalisar Wakilai ta sanya Laraba, 26 ga watan Fabrairu, a matsayin ranar da za ta buɗe zauren sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin dokokin haraji.
Kakakin Majalisar, Abbas Tajudeen wanda ya bayyana hakan a ranar Talata, ya ce za a gudanar da sauraron ra’ayin jama’ar a zauren majalisar na wucin-gadi.
Abba ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaro ta Kano Za a binciki INEC kan jinkirin gudanar da zaɓen cike giɓiYa bayyana cewa, kwamitin majalisar kan harkokin kuɗi ne zai jagoranci zaman sauraron ra’ayin jama’ar haɗi da wasu ƙusoshin majalisar na wasu kwamitocin.
Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne ƙudirin kafa dokokin harajin guda huɗu da Shugaba Bola Tinubu ya aike wa majalisar suka tsallake karatu na biyu.
Wannan zaman sauraron ra’ayin da za a gudanar zai ba da damar karɓar shawarwarin masu ruwa da tsaki domin ji daga gare su dangane da ƙudirin Dokar Harajin da aka riƙa kai ruwa na a kai a faɗin ƙasar.
Idan ba a manta ba, a farkon watan Janairun da ya gabata ne gwamnonin Nijeriya suka fitar da sabon tsari na rabon haraji a ƙasar, bayan wata ganawa da suka yi da kwamitin da aka kafa domin yin nazari kan ƙudurin sabuwar dokar haraji ta ƙasar.
Tun a ƙarshen shekarar da gabata ce Tinubu ne ya gabatar wa Majalisar Tarayyar ƙudurin aiwatar da gyaran fuska ga dokar harajin, lamarin da ya haifar da zazzafar muhawara da raba kawunan shugabanni a ƙasar.
Haka ne ya kai ga cewa shugaba Tinubu da Majalisar Dokokin Tarayya sun jingine batun muhawara da amincewa da dokar har sai bayan an sake yin nazari a kanta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dokar Haraji Majalisar Wakilai Ra ayin jama a
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Bola Ahmed Tinubu A Tarayyar Najeriya Ya Bada Umurnin A Gudanar Da Bincike Kan hatsarin Daren Laraban da Ta Gabata A Abuja
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bada umurnin a gudanar da bincike don gano abinda ya hadda hatsarin day a faru a kan gadar Karuk an titin Abuja Keffi a daren Labaran da ta gabata, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da kuma jikatan wasu.
Jaridar Premium Times ta nakalto shugaban kasar yana fadar haka tabakin mai bashi shawara kan al-amuran watsa labarai Bayo Onanuga a jiya Alhamis.
Shugaban ya bayyana alhininsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma fatan murmurewar wadanda suka ji rauni. Ya kuma bukaci a gaggauta gudanar da bincike don sanin abinda ya haddasa hatsarin day a kai da wannan asarar, don daukar matakan hana aukuwar irinsa nan gaba.