Kasar Sin Ta Mayar Da Martani Ga Tattaunawar Amurka Da Rasha Kan Rikicin Ukraine
Published: 19th, February 2025 GMT
Kasar Sin na maraba da duk kokarin da ake yi cikin lumana don warware rikicin kasar Ukraine, ciki har da tattaunawa tsakanin Amurka da Rasha, kuma Sin na fatan dukkan bangarori da masu ruwa da tsaki za su shiga cikin shawarwarin samar da zaman lafiya in lokaci yayi.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na yau Talata, yana mai cewa, ko da yaushe kasar Sin tana da yakinin cewa, tattaunawa da yin shawarwari, ita ce hanya daya tilo da za a iya warware rikicin, kuma ta himmatu wajen inganta shawarwari don samar da zaman lafiya.
Ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga wata tambaya game da ganawar da jami’an Amurka da na Rasha suka yi a ranar Talata a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, ba tare da halartar Ukraine ba. (Mohammed Yahaya)
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Yemen Sun Kakkabo Jirgin Yakin Amurka Wanda Ake Sarrafa Shi Daga Nesa Na 19
Sojojin kasar Yemen sun kakkabo jirgin yakin Amurka wanda ake sarrafashi daga nesa samfurin MQ-9 na 19 a jiya Lahadi da yamma a sararin samaniyar kasar.
Tashar talabijan ta Presstv daga nan Tehran ya bayyana cewa sojojin kasar ta Yemen sashen UAV wato masu kula da abinda ake kira ‘Drones’ sun bada sanarwan kakkabo jirgin yaki na Amurka ne a lokacinda yake tattara bayanai a wasu yankuna a sararin samaniyar kasar.
Masana sun bayyana cewa farashin ko wane jirgi yakin samfurin MQ-9 ya kai dalar Amurka miliyon $33, don haka ya zuwa yanzu kasar Amurka ta yi asarar dalar Amurka miliyon $600. Kafin haka dai sojojin Yemen bangaren makamai masu linzami sun bada sanarwan cilla makamai masu linzami samfurin Balistic guda biyu kan HKI, wanda ya kai ga rufe tashar jiragen sama na Bengerion a birnin Yafa (telaviv.) . Bugediya Yahyah Saree kakakin sojojin kasar ta Yemen ya bayyana cewa godiya ta tabbata ga All..saboda dukkan makaman sun cimma manufofin cillasu, wadanda suka hada da rufe tashar jiragen sama na Bengrion da tilastawa miliyoyin yahudawan sahyoniyya gudu zuwa wuraren buya.
Saree ya kammala da cewa, ayyukan soje a kan HKI da kuma Amurka zasu ci gaba har zuwa dakatar da yaki a Gaza.