Jagora Ya Gana Da Shuwagabannin Kungiyar Jihadul Islami A Nan Tehran
Published: 19th, February 2025 GMT
Jagoran juyin juya halin Musulunci A nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya gana da shuwagabannin kungiyar Jihadul Islami na kasar Falasdinu da aka mamaye a jiya Talata.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Ziyad Nakhalah shugaban kungiyar ne ya jagoranci tawagar kungiyar zuwa ganawa da jagoran.
Labarin ya nakalto Jagoran juyin juya halin musulunci ya fadar cewa a halin yanzu babu wani abunda HKI zata yi a gaza sai idan kungiyoyi masu gwagwarmaya suna sun abin ya faru, saboda kekkyawar riko da suka yiwa yankin.
Imam Seyyed Ali Khamenei, ya yabawa kungiyoyin falasdinawa kan hadin kai da suka nuna a yankin da ya gabata.
Ziyad al-Nakhalah, babban sakataren kungiyar Jihad Islami, ya bayyana cewa sun zo gaban Rahbar ne don tattauna mataki nag aba da yakamata su dauka a halin da ake ciki a kasar Falasdinu da aka mamaye.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Firaministan Kasar Sin Ya Gana Da Sanata Steve Daines
A yau Lahadi firaministan kasar Sin Li Qiang, ya gana da dan majalisar dattawan Amurka sanata Steve Daines, tare da wasu ‘yan kasuwan Amurka da suka zo kasar Sin, don halartar dandalin bunkasa kasa na Sin na shekarar nan ta 2025 wanda ya gudana a nan birnin Beijing. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp