Mutane Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Wani Abu A Kasuwar Zamfara.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan daba sun hallaka matashi ana sallar Tahajjud a Kaduna

Wasu da ake kyautata zaton ’yan daba ne sun kai hari wani masallaci da ke yankin Rigasa a Jihar Kaduna, inda suka kashe wani matashi yayin da ake tsaka da sallar Tahajjud.

Sai dai rundunar ’yan sandan jihar, sun kama mutum 12 da ake zargi da hannu a kai hari masallacin.

Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia An wawushe motar abinci ta Hukumar WFP a Borno

Kakakin rundunar, Mansir Hassan, ya ce ’yan daban sun fito daga unguwanni daban-daban kamar Malalin Gabas, Tudun Wada, Rafin Guza, da Unguwar Baduko.

Sun kai farmaki Masallacin Layin Bilya, titin Makwa a Rigasa da misalin ƙarfe 2 na dare yayin da masu mutane ke sallar Tahajjud.

Kafin jami’an tsaro su isa wajen, sun sun daɓa wa wani matashi mai shekara 28, Usman Mohammed, wuƙa har lahira.

Rundunar tare da haɗin gwiwar JTF sun ɗauki mataki cikin gaggawa, inda suka kama mutum 12 kuma ana bincike a kansu.

Haka kuma, an samu makamai a hannu waɗanda aka kama.

An fara bincike domin gano gaskiyar lamarin da tabbatar da cewa an hukunta waɗanda suka aikata laifin.

Sakamakon haka, ’yan sanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a wuraren ibada da sauran wuraren da ake ganin za su iya fuskantar barazana.

Hukumomi sun buƙaci al’umma da su kasance masu sanya ido tare da gaggauta kai rahoto idan sun ga wani abun zargi.

’Yan sanda sun kuma gargaɗi masu aikata laifi da su daina ko su fuskanci hukunci mai tsanani.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gobara ta tashi a gidan mai sakamakon fashewar tanka a Neja
  • ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a Zamfara
  • Matasa sun kashe yaron da suka yi garkuwa da shi a Bauchi
  • An Kashe Askarawa 6 da ‘Yan Sa-kai 4 A Zamfara 
  • Isra’ila ta kashe wani mamba na ofishin siyasa na Hamas
  • Kao Kim Hourn: Ba Ta Hanyar ‘Siddabaru’ Kasar Sin Ta Cimma Nasarori A Fannin Ci Gaba Ba Sai Dai Ta Hanyar Aiki Tukuru Kuma Mai Dorewa
  •  “Yan Ta’adda Sun Kai Hari Akan Masu Salla A Jamhuriyar Nijar
  • Chelle Ya Fara Da Ƙafar Dama A Super Eagles 
  • GMBNI Ta Yi Allah-wadai Da Kisan Gillar Wani Almajiri A Jihar Jigawa
  • ’Yan daba sun hallaka matashi ana sallar Tahajjud a Kaduna